Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba
- Wani mutum yayi zargin matar dansa da lalata har ya fara tunanin yaran da suka haifa guda uku ba na dansa bane
- Wannan dalilin ya sanya ya lallaba asibiti don gwajin DNA na tabbatar da yaran dan nasa ne, sakamako da ya gigita shi
- Sai dai, sakamakon ya nuna cewa yaran dansa ne, amma kuma ba shi bane uban mahaifinsu na asali
Wani mutum wanda yayi yunkurin tozarta matar dansa da zargin tana ha'intarsa ya kwashi kashinsa a hannu, The Nation ta wallafa.
Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba yayi zargin cewa matar dansa tana lalata da wasu mazajen a waje, dalilin haka ta haifa masa yara uku da ba jikokinsa na asali bane. Tuni ya tilasta su garzayawa asibiti don gwajin DNA a san gaskiyar lamarin.
Sai dai, bayan sakamakon asibitin ya fita an gano cewa tabbas yaran mutumin ne amma kuma, mahaifinsu ba dansa bane.
KU KARANTA: In har liyafar badala ta sa aka rushe otal, gidan dan El-Rufai ya dace a fara rushewa, Reno Omokri
Wannan al'amarin ya janyo tashin hankali kwarai sakamakon kiyayyar dake tsakanin mutumin da matar dan nasa.
Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Drpenking ya wallafa labarin kamar haka:
"Wani siriki da ya tsani matar dansa ya lallaba asibiti don gwajin DNA a kan shi da jikokinsa don a tabbatar da halascinsu.
"Sai dai, sakamako ya nuna cewa ba jininshi bane su. Da aka cigaba da bincike sai aka gano cewa mahaifinsu ba dan shi bane."
KU KARANTA: Kyakyawar budurwa lauya ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare (Hotuna)
A wani labari na daban, Farfesa Khalifa Dikwa, daya daga cikin dattawa a kungiyar dattawan Borno ya nuna damuwarsa a kan hauhawar rashin tsaro a yankin.
Ya ce baya da babban birnin jihar Borno, babu inda mutane ke rayuwa da tsaro a fadin jihar.
"Ko da a ce babu Boko Haram a wasu wurare, sun riga sun tsorata jama'a kuma suna zukatan jama'a tare da hana su zaman lafiya," Dikwa ya sanar da Channels TV a wani shirin daren ranar Litinin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng