In har liyafar badala ta sa aka rushe otal, gidan dan El-Rufai ya dace a fara rushewa, Reno Omokri
- Reno Omokri ya yi martani ga gwamnan jihar Kaduna a kan rushe otal din Asher da yayi
- Ya zargi gwamnan da yin abu kai tsaye ba tare da duba shari'a ba ko wata dokar jihar
- Ya shawarci gwamnan da ya fara rushe gidan dansa kafin ya kai ga hana liyafar badala
Reno Omokri ya yi martani a kan rushe otal din da gwamnatin jihar Kaduna tayi sakamakon zargin zama wurin da za a yi liyafar badalar da wasu samari suka shirya.
A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke mashiryan wata liyafar badala yayin da gwamnatin jihar ta rushe inda ake zargin za a yi liyafar.
A yayin martani game da rushe ginin, Omokri ya ce kamata yayi gwamnatin jihar ta rushe gidan dan gwamnan jihar.
KU KARANTA: Kyakyawar budurwa lauya ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare (Hotuna)
Ya wallafa: "Idan har liyafar badala ta sa aka rushe otal, toh kamata yayi Nasir El-Rufai ya fara rushe gidan dansa da farko.
"Dukkanmu dai mun ga yadda yayi barazanar taruwa da abokansa su yi wa mahaifiyar wani dan kabilar Ibo fyade. Wannan kuwa ta fi liyafar badala.
"Lamarin yana bayyana rashin doka a Kaduna. Ba wai ina goyon bayan yin liyafar bane, amma shin liyafar badala haramun ce a kundin tsarin mulkin kasar nan?
''Kasar ce fa wani Sanata ya auri yarinya mai shekaru 13 yayin da wani ya tsinka wa wata mata mari inda yaje siyan butuntumin jima'i"
KU KARANTA: Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC
A wani labari na daban, Iklima Musa tana neman a karbar mata hakkinta daga wurin kishiyarta wacce ta watsa mata tafasasshen ruwa a jihar Filato, Linda Ikeji ta wallafa.
Idan za mu tuna, wacce ake zargi da aika-aikar mai suna Justina Peter ana nemanta ido rufe bayan lamarin da ya faru a Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
An gano cewa matar bata taba shiri da Iklima ba tun bayan da mijinta ya aurota a matsayin mata ta biyu a shekaru uku da suka gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng