CPS: Gwamnatin Tarayya ta warewa ‘yan fansho kudin da su ke bi N11.82bn

CPS: Gwamnatin Tarayya ta warewa ‘yan fansho kudin da su ke bi N11.82bn

- Hukumar PenCom tace za ta biya ‘yan wasu fansho Naira biliyan 11.82

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a fito da wadannan kudi

- Za a biya ma’aikatan da su kayi aiki, su kayi ritaya kafin shekarar 2004

Gwamnatin tarayya ta fitar da Naira biliyan 11.82 da nufin a biya tsofaffin ma’aikata hakkokin da su ke bi a karkashin tsarin fansho na CPS.

Jaridar Daily Trust ta ce za a biya tsofaffin ma’aikatu da su ka yi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya shekarun da suka wuce.

Babban jami’in hukumar kula da fansho na kasa ta PenCom, Peter Aghahowa, ya bayyana wannan a ranar Laraba, 6 ga watan Junairu.

Mista Peter Aghahowa ya ce kudin da aka fitar ya kunshi hakkokin ma’aikatan da su kayi wa gwamnati aiki har zuwa watan Yunin 2004.

KU KARANTA: Samari da ‘Yan mata suna so a kashe lefe da kayan aure a kasar Hausa

Aghahowa yake cewa a wannan lokaci ne gwamnati ta shigo da dokar fansho na kasa a Najeriya.

Jawabin ya ce: “Hukumar (PenCom) ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya na ganin an fito da hakkokin tsofaffin ma’aikata, za a biya su.”

“Mun godewa tsofaffin ma’aikatan gwamnatin da abin da ya shafa da su kayi hakuri.” Inji sa.

Idan za ku tuna a watan Agustan shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta bukaci a ware N14.92 da nufin a biya wasu tsofaffin ma’aikatan kasar.

KU KARANTA: Gwamnan Kwara ya soma 2021 da fatattakar duka Mukarrabansa

CPS: Gwamnatin Tarayya ta warewa ‘yan fansho kudin da su ke bi N11.82bn
Shugaba Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hukumar PenCom ta bayyana cewa za a yi amfani da kudin da aka ware ne wajen biyan tsofaffin ma’aikatan kasar bashin kudinsu na watanni hudu.

Legit.ng Hausa ta fitar da rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara kudin shan wutar lantarki sau uku daga shekarar 2016 zuwa 2021.

Karin kudin wuta biyu shugaba Muhammadu Buhari ya yi kafin sabon karin da aka yi a 2021.

Hukumar NERC mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da sauyin da aka samu wajen shan wuta daga ranar 1 ga watan Junairu, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel