Jerin karin farashin wutar lantarki da aka yi a Najeriya daga 2016 zuwa yanzu
- Daga 2015 zuwa yanzu, anyi karin farashin wutar lantarki har uku a Najeriya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin farko ne a cikin 2016
- An kuma shiga wannan sabuwar shekara ta 2021 da sauyin farashin lantarkin
Hukumar NERC mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da sauyin da aka samu wajen shan wuta daga ranar 1 ga watan Junairu, 2020.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wannan ne karo na uku da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara kudin wuta a shekara biyar.
A shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin wuta na MYTO da sama da 50%.
A ka’ida ya kamata hukuma ta rika nazarin kudin shan wuta na MYTO sau biyu a shekara, ta yadda farashin zai rika sauka kasa ko kuma ya tashi sama.
KU KARANTA: Lantarki a Najeriya talaka sai dai hakuri - Kyari
Kamar yadda wani babban jami’in hukumar NERC, Michael Faloseyi, ya bayyana, an yi wannan kari ne a dalilin tashin farashin da kaya su ka yi a Najeriya.
Bayan watanni hudu sai gwamnati ta sake amincewa da wani karin kudin lantarkin a watan Yunin 2016 duk da darajar Dala da farashin kaya ba su tashi ba.
Hukumar NERC ta yi yunkurin kara kudin shan wuta a watan Afrilun 2020, amma ta dakatar da maganar zuwa tsakiyar shekara saboda annobar Coronavirus.
A Satumban 2020 aka dawo da maganar karin kudin lantarkin, amma dole aka hakura da wannan shiri sai karshen shekara, aka tabbatar da karin kudin.
KU KARANTA: Tashar wuta ta lalace, jama'a sun shiga duhu
A watan Junairun nan ne aka amince da kari na uku da aka yi wa mutanen Najeriya. Ana tunani nan da watan Yunin 2021 za a sake bijiro da maganar wani karin.
A jiya ne karamin Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo ya yi karin haske game da rahotannin tashin farashin kudin shan lantarki da aka cewa an yi.
Festus Keyamo SAN ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi karin shan kudin wutar lantarki ba.
Karamin Ministan tarayyar yace abin da aka yi ba karin farashi bane. Keyamo ya bayyana cewa kamfanoni sun yi wa farashin wasu ‘yan kwaskwarima ne kurum.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng