'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 har lahira a Katsina
- 'Yan sanda sun samu nasarar kashe 'yan bindiga 6 a jihar Katsina ranar Laraba
- Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Gambo Isah ne ya sanar da hakan ta wata takarda
- A cewarsa, 'yan sandan sun samu nasarar kwace miyagun makamai da dama a hannunsu
A wata takarda da kakakin hukumar 'yan sanda, Gambo Isah ya saki, ya tabbatar da yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga 6 a jihar Katsina.
'Yan sandan sun kai samame ne a ranar 1 ga watan Janairun 2021, inda suka samu nasarar kwatar miyagun makamai kamar bindigogi kirar G3, AK 47, LAR, bindigogin toka guda biyu da 10 rounds na 7.62mm ammunition a hannunsu.
"A ranar 2/1/2021 sun samu nasarar kwatar AK 47 da 32 rounds na 7.62mm ammunition a Pauwa Bushland dake karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina," a cewarsa.
KU KARANTA: Fitattun mutane10 da rasuwarsu ta matukar girgiza jihar Katsina a 2020
"Sannan ranar 3/01/2021 da misalin karfe 3am, 'yan fashi sun kai farmaki kauyen Mahuta da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina amma mutane sun yi karfin halin dakatar dasu, inda suka kwace bindigogi kanana guda 2 a hannunsu."
Wannan al'amarin ya biyo bayan ceto mutane 23 da 'yan sanda da wasu jami'an tsaro suka taru suka yi a kauyen Lambo dake karamar hukumar Kurfi dake jihar.
Yayin kokarin ceto mutanen, 'yan sandan sun samu nasarar harbe 'yan ta'adda 6, inda suka kwato dabbobi 74 da babura 12.
KU KARANTA: Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci
A wani labari na daban, annobar korona ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.
Hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta sanar da komawa biyan ma'aikatanta karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da ta fara bayan boren da kungiyar kwadago tayi, The Cable ta ruwaito.
A yayin tabbatar da wannan cigaban, mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng