Fitattun mutane10 da rasuwarsu ta matukar girgiza jihar Katsina a 2020

Fitattun mutane10 da rasuwarsu ta matukar girgiza jihar Katsina a 2020

- Kowanne dan Adam sai ya dandana mutuwa

- Jihar Katsina ta dandana radadin rashin fitattun mutane a 2020

- Daga cikinsu akwai 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sarakunan gargajiya

Mutuwa riga ce bata fita kamar yadda bahaushe ke cewa. Duk wani mai rai mamaci ne kuma kowa sai ya dandana dacin mutuwa.

A shekarar 2020, jama'a da dama a jihar Katsina manya sun rasa rayukansu, lamarin da ya matukar girgiza zukatan jama'a.

Katsina Post ta jero sunayen manyan mutane 10 fitattu a jihar Katsina da suka rasu a 2020.

Daga cikinsu akwai masu sarautar gargajiya, 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauransu.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna

1. Sada Ilu

Ya yi takarar kujerar gwamna sau biyu a karkashin jam'iyyar APC kuma sau daya a karkashin jam'iyyar PDP. Ya rasu a sa'o'in farko na ranar Lahadi, 12 ga watan Janairun 2020.

2. Ibrahim Maikaita Bako

Shine alkalin da ke shugabantar shari'ar zargin badakalar tsohon Gwamnan Katsina Shema. Ya rasu a sa'o'in farko na ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2020.

3. Alhaji Tukur Usman Sa'idu Faskari

Shine hakimin Faskari kuma Sarkin Yamman Katsina. Ya rasu a ranar Juma'a 24 ga watan Janairun 2020.

Wata majiya kusa da iyalinsa ta tabbatar da cewa ya rasu a Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya.

4. Group Captain Abubakar Abe

Shi ke da mukamin Jarman Katsina kuma hakimin Tsiga. Ya rasu a ranar 11 ga watan Fabrairun 2020.

KU KARANTA: Bidiyon budurwa gurfane tana kuka a gaban saurayi a titi ya janyo cece-kuce

Mace-mace 10 da suka matukar girgiza jihar Katsina a 2020
Mace-mace 10 da suka matukar girgiza jihar Katsina a 2020. Hoto daga Katsinapost.com.ng
Asali: UGC

5. Hon Abdurrazak Ismaila Tsiga

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar jihar Katsina. Ya rasu a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2020.

6. Alhaji Garba Lado Danmarke

Shi ne mahaifin fitaccen dan siyasa Sanata Yakubu Lado Danmarke. Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jama'iyyar PDP . Ya rasu a ranar 20 ga watan Mayun 2020.

7. Alhaji Atiku Maidabino

Wasu 'yan bindiga a ranar 1 ga watan Yunin 2020 sun kai farmaki garin 'Yan Tumaki da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina.

A ranar suka kashe Maidabino wanda shine hakimin garin.

8. Mallam Samaila Isah Funtua

Shine manajan daraktan jaridar Democrat kuma dattijo a jihar Katsina. Ya rasu a ranar 20 ga watan Yulin 2020.

9. Malam Wada Maida

A ranar 17 ga watan Satumban 2020 ne jihar Katsina ta tashi da labarin rasuwan tsohon sakataren yada labarai na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

10. Farfesa Ali Muhammad Garba

Malami ne a jami'ar Bayero da ke Kano amma dan asalin jihar Katsina. Ya rasu a ranar 6 ga watan Disamban 2020.

KU KARANTA: Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci

A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa sun cimma ajalinsu sakamakon samamen tudu da na jiragen yaki da soji suka kai musu a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a jihar Kaduna, Vanguard ta wallafa.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya ce dakarun sun tabbatar da samamen da suka kai a ranar Litinin a Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau, Fadama kanauta, Galadimawa, Kaya, Kidandan, Yadi, Dogon Dawa, Ngede Allah, Damari, Saulawa, Takama, Kuduru, Ungwan Yakoda babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"An ga 'yan bindiga a Yadi kuma an ragargaji yankin ta sama sannan an kashesu da yawansu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: