Anyi garkuwa da mutum 20, an kashe mutum daya a Nasarawa

Anyi garkuwa da mutum 20, an kashe mutum daya a Nasarawa

- Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 20 tare da kashe mutum daya a kauyen Gwari-Gadabuke a jihar Nasarawa

- Rundunar yan sanda ta karyata rahoton, inda tace sun gano gawar mutum daya amma basu da labarin garkuwa

- Rahman Nansel, kakakin yan sandan jihar ya ce sun dakile wani yunkurin fashi tare da kashe wani da ake zargi a karamar hukumar Lafia

An ruwaito cewa an kashe mutum daya, jiya, tare da yin garkuwa da mutane 20 da wasu yan bindiga suka yi a kauyen Gwari-Gadabuke, da ke karamar hukumar Toto a Jihar Nasarawa, The Punch ta ruwaito.

Mutum 20 din da aka yi garkuwa dasu an ruwaito cewa suna tafe cikin motoci 3 yayin da aka kashe tsohon sakataren ilimi na karamar hukumar Nasarawa, Mallam Salihu a yayin da suke tafiya zuwa Toto daga Nasarawa.

Anyi garkuwa da mutum 20, an kashe mutum daya a Nasarawa
Anyi garkuwa da mutum 20, an kashe mutum daya a Nasarawa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun kai hari Monguno

Sakataren masarautar Gadabuke, Abdullahi Baba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yan bindigar sun fito da yawan su daga daji tare da kai hari kan abubuwan hawan da ke zirga-zirga a titin inda suka yi garkuwa da mutane 20 daga motocin haya guda uku.

An gano gawar tsohon sakataren ilimin wanda ya ke tare da abokan sa a motar gida a wata lalatacciyar mota, su kuma sauran ba a san inda aka tafi da su ba.

Da yake bayani, mai magana da yawun yan sanda, Rahman Nansel, ya karyata rahoton, inda ya ce iya gawa aka tsinta a wata lalatacciyar motar Rovers da wayoyin hannu kirar Tecno.

KU KARANTA: Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

"Yan sanda ba su tabbatar da garkuwa da mutane 20 ba," inji kakakin yan sandan.

Bugu da kari, Nansel ya tabbatar da cewa rundunar ta dakile yunkurin fashi, ta kore tare da kashe wani da ba a san kowaye ba da ake zargi a Gidan Gambo, lokacin da suka tare titi a karamar hukumar Lafia da nufin yin fashi.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel