Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

- Bidiyon mai martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya janyo cece kuce a dandalin sada zumunta

- An hoton bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna shi tare da matan zumunta suna wakokin addini

- Mutane da dama sunyi ta bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon inda wasu suka yabe shi wasu kuma akasin haka

Wani hoton bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya janyo hankulan 'yan Najeriya musamman masu amfani da Twitter.

A cikin bidiyon, An gano Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, yana rere wakokin yabo na addinin kirista tare da 'matan zumunta' a yayin da suka kai masa ziyara fadarsa.

Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce
Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce. Hoto: @EditiEffiong
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter

Kungiyar fitaciyyar kungiya ce ta masu waka a Kiristocin arewacin Najeriya da aka san su da iya rere wakokin addinin kirista masu ratsa zuciya.

Isa Gusau, babban sakataren watsa labarai na gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum, ne ya wallafa bidiyon kuma a halin yanzu fiye da mutane 1000 sun latsa alamar so kan bidiyon.

Ba a san tabbacin ranar da aka nadi bidiyon ba amma a garin Gusau aka dauka kamar yadda fitaccen manhajar sadarwa ta WhatsApp ta nuna.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

Dakta Adamu shine sarki na 11 a masarautar Bauchi kuma sarki mai ci a yanzu. Ya yi karatun digirin farko a Fasahar Gini daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Wasu da dama sun yaba wa abinda sarkin ya yi inda suka ce hakan na iya hada kan al'ummar jihar da kasa baki daya.

A wani labarin, gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Litinin ya aza harsashin gina jami'ar Al-Ansar, jami'a ta farko mai zaman kanta a jihar.

Zulum wanda gwamnatin sa ta bada fili mai girman hekta 100 ga gidauniyar Al-Ansar don gina jami'ar, ya kuma umarci da a gina titi mai nisan kilo mita 2.3 da kuma bohol a jawabin da ya gabatar wajen taron.

Zulum ya kuma umarci ma'aikatar ilimi mai zurfi da su bibiyi wanda ya samar da jami'ar don ganin yadda gwamnati zata iya ci gaba da tallafawa aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: