Wutar Lantarki ta manya ce kawai a kasar nan talakawa sai dai hakuri - Mele Kyari

Wutar Lantarki ta manya ce kawai a kasar nan talakawa sai dai hakuri - Mele Kyari

- Babban manajan daraktan matatar man fetur ta Najeriya, Mele Kyari ya nuna damuwar shi ta yadda rashin wutar lantarki ya yi katutu a kasar nan

- Babban manajan ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na fafutukar neman abin sakawa a bakin salati amma wutar lantarki ta gagaresu

- Ya ce akwai bukatar Najeriya ta mike tsaye don ganin ta shawo kan kalubalen rashin wuta da kasar nan ke fuskanta

Babban manajan daraktan matatar man fetur ta Najeriya, Mele Kyari ya nuna damuwar shi ta yadda rashin wutar lantarki ta yi katutu a kasar nan.

A yayin jawabi a taron tattalin azrki na man fetur din Najeriya wanda hakan har ta kai ga sun saka hannun kan wasu makuden kudi da USTDA ta bada don aikin wutar lantarki a Abuja a ranar Talata, shugaban ya jajanta yadda ‘yan Najeriya ke fafutukar samun abin sakawa a bakin salati sannan kuma suke neman wutar lantarki. Ya ce wutar lantarkin ta zamo ta masu hannu da shuni.

Kyari ya ce kalubalen rashin wuta a Najeriya dole ne a shawo kanshi a gaggauce, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Buhari ya san wadanda suke rike da Leah Sharibu - Kungiyar Kiristoci

Ya ce: “Ga wannan kasar da ma wasu da ke Hamada a Afirka, abinda kullum muke tunani shine abinci. Akwai mutane da yawa da basu iya cin abinci ko sau daya. Hakazalika kuwa wutar lantarki ta zama abin jin dadi kuma masu kudi ke samu.

“Mafarkin kowa ne ya mallaki janareto ko dan karami ne. Dole ne mu samo hanyar shawo kan rashin wutar lantarki da gaggawa. Mun san muna da iskar gas mai yawa kuma dole ne mu kirkiri ababen more rayuwa ta hanyar amfani da gas din.

“Dole ne su samu lantarki don samar da ayyukan yi da arziki mai yawa. Ta haka ne zamu samu zaman lafiya a kasar nan.”

A wani bangaren daban kuma kasar Amurka ta sanar da cewa za ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 40 a matsayin taimako ga jama'ar kasar da ta'addancin 'yan Boko Haram ya shafa.

Mike Pompeo, sakataren kasar ne ya sanar da hakan a ranar Talata a birnin Washington DC a yayin wani taro tare da ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, in ji jaridar The Cable.

Wannan ci gaban ya biyo baya ne cikin kwanaki hudu da kasar Amurka ta haramtawa 'yan Najeriya Visa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel