'Yan ta'adda sun kai hari Monguno

'Yan ta'adda sun kai hari Monguno

- Yan ta'adda sun kai hari garin Monguno da sanyin safiyar Talata sai dai babu takamaimai adadin wanda harin ya shafa

- Hukumar Red Cross ta ce tana jinyar mutane uku ciki harda yaro dan shekara biyar

- Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, sai dai anfi alakanta shi ga ISWAP

Wani karamin gungun 'yan ta'adda a ranar Talata sun kai hari garin Monguno, a karamar hukumar Monguna da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya.

Ba a bayyana takamaiman adadin da suka jikkata ba, amma an ruwaito cewa mutane kalilan sun samu raunika, a cewar rahoton HumAngle.

'Yan ta'adda sun kai hari Monguno
'Yan ta'adda sun kai hari Monguno. Hoto @EFillion
Asali: Twitter

Monguno mai nisan kilo mita 130 daga arewa maso gabashin Maiduguri, babban birnin jihar, yana daya daga cikin manyan garuruwan da cibiyoyin jami'an tsaro, gidajen jami'ai, sansanin gajiyayyu da yan gudun Hijira a arewacin Borno.

DUBA WANNAN: Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa harin da aka kai Monguno, garin Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da misalin 4 na asuba.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa HumAngle cewa harin bai ta'azzara ba saboda bai kunshi yan ta'adda da yawa ba idan aka kwatanta da harin Janairun bara.

Wannan abin damuwa ne, yan ta'adda na kai hari garuruwan da sansanonim jami'an tsaro su ke.

A wani da ya wallafa a shafi Twitter, da yammacin Talata, Eloi Fillion, shugaban hukamar bada agajin gaggawa ta RedCross (ICRC) ya ce kungiyar tana jinyar mutane uku wanda suka ji ciwo lokacin harin, ciki harda yaro dan shekara biyar.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

A watan Yuni 2020, yan ta'adda dauke da miyagun makamai, kananan bindigu da kuma tanka suka kai hari kan jami'an tsaro da kuma sansanin yan gudun hijira da ke garin.

A wata sanarwa da majalisar dinkin duniya ta fitar, "jami'an kariya da aka girke a sansanin kula da marasa karfi sun bada kariya ga ma'aikata fiye da hamsin da ke aiki a lokacin da aka kawo harin."

Duk da cewa har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na ranar Talata, karamar hukumar Monguna na daga cikin kananan hukumomin jihar Borno da kungiyar ISWAP ta ke yawan kai hare hare.

A wani labarin kuma, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel