JAMB ta bude yin rajistar sunayen masu shiga na 2020/2021

JAMB ta bude yin rajistar sunayen masu shiga na 2020/2021

- JAMB ta fitar da muhimmiyar sanarwa kan tsarin shiga na 2020/2021

- JAMB ta ce cibiyoyi da suka hada da makarantun ilimin kere-kere da kwaleji na ilimi yanzu na iya shigar da sunayen wadanda aka zaba

- Hukumar ta bayyana cewa a guji labarin da bai fito daga magatakardar hukumar a kan rajistar 2021

Hukumar Jarrabawar Shiga Jami'a (JAMB) ta sanar da bude kofar daga cibiyoyi don daura sunayen wadanda aka zaba domin shiga 2020/2021.

Magatakardar hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede ne ya sanar da hakan a Abuja a ranar Talata, 5 ga Janairu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamitin ya ce duk tsarin shigar dole ne ya bi ta cikin Tsarin Gudanarwa da Shiga Kasa (CAPS) don amincewa.

KU KARANTA: Ma'aikata sama da 300 ba a biyansu albashi a Majalisar Dokoki

JAMB ta bude yin rajistar sunayen masu shiga na 2020/2021
JAMB ta bude yin rajistar sunayen masu shiga na 2020/2021 Credit: The Guardian
Source: Facebook

“Ku lura kuma cewa shiga bawai kawai ga jami’o’i bane. Akwai kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi amma ban da wadanda a ka rufe saboda COVID-19, yajin aikin bai shafe su ba."

A halin yanzu, JAMB ta ce ba ta fara sayar da fom din Unified Tertiary and Matriculation Examination (UTME) na 2021 ba.

Hukumar jarrabawar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu, ta hanyar sanarwa ta mako-mako na ofishin magatakardan.

JAMB ta kuma gargadi masu son yin jarrabawar da su yi hattara da masu yada jita-jita da masu damfara, ya kara da cewa bayanin ya zama dole saboda labaran karya.

Hukumar shirya jarabawar ta kuma danganta jinkirin sayar da fom din ga rikicin COVID-19 da ya mamaye kasar nan.

KU KARANTA: Da alamun za a je aikin Hajji bana

JAMB, duk da haka, ta bayyana cewa za ta kammala shirye-shirye nan ba da jimawa ba kan sayar da fom din.

A wani labarin, Wannan sanarwar na kunshe cikin wani sako da Fabian Benjamin, kakakin Hukumar shirya jarabawar neman shiga jami'a da makaratun gaba da sakandire ya fitar a ranar Litinin.

A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, Hukumar JAMB a makon jiya ne ta kayyade 160, a matsayin mafi karancin makin samun shiga jami'a da makarantun gaba da sakandire na gwamnati.

Hukumar ta cimma matsayar hakan ne bayan wani tsari na jefa kuri'a da ta gudanar, sai dai wasu jami'o'in sun ce ba za su dauki daliban da makinsu ya yi kasa da 180 ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel