Jami'o'i sun kayyade makin samun gurbin karatu a bana - JAMB
Kimanin makarantu masu bayar da shaidar digiri 51 a Najeriya, ba za su dauki duk dalibin da ya samu maki kasa da 180 ba a jarabawar JAMB ta shekarar 2020.
Wannan sanarwar na kunshe cikin wani sako da Fabian Benjamin, kakakin Hukumar shirya jarabawar neman shiga jami'a da makaratun gaba da sakandire ya fitar a ranar Litinin.
A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, Hukumar JAMB a makon jiya ne ta kayyade 160, a matsayin mafi karancin makin samun shiga jami'a da makarantun gaba da sakandire na gwamnati.
Hukumar ta cimma matsayar hakan ne bayan wani tsari na jefa kuri'a da ta gudanar, sai dai wasu jami'o'in sun ce ba za su dauki daliban da makinsu ya yi kasa da 180 ba.
Daga cikin makarantu 51 da su ka yanke shawara kan 180 a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatu, guda daya ce kadai ta kayyade 210 a matsayin mafi karancin makin da ta ke bukata.
KARANTA KUMA: Ma'aikatan Gwamnati a jihar Oyo sun koma aiki
Wasu jami'o'in 9 kuma sun riki 200 a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatunsu a duk kwasa-kwasai.
Haka kuma wata jami'a guda daya, ta kayyade 190 a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatu, yayin da wasu jami'o'in 40 suka takaita a kan maki 180.
Jerin jami'o'in da ba za su karbi kasa da maki 200 ba:
1) Jami'ar Pan-Atlantic - 210
2) Jami'ar Covenant - 200
3) Jami'ar Obafemi Awolowo - 200
4) Jami'ar Ibadan - 200
5) Makarantar Koyon Kwarewa a Limancin Addinin Kirista ta All Saints - 200
6) Jami'ar Benin - 200
7) Makarantar Koyon Kwarewa a Limancin Addinin Kirista ta Bigard Memorial - 200
8) Jami'ar Lagos - 200
9) Kwalejin Koyon Ilimin Addinin Kiristanci ta Immanuel - 200
10) Makarantar Koyon Kwarewa a Limancin Addinin Kirista ta St. Peter and Paul - 200
Jerin jami'o'in da ba za su karbi kasa da maki 190 ba:
11) Jami'ar Jihar Legas - 190
Jerin jami'o'in da ba za su karbi kasa da maki 180 ba:
12) Jami'ar Sojin Kasa, Maiduguri - 180
13) Jami'ar Jihar Ekiti - 180
14) Jami'ar Afe Babalola - 180
15) Kwalejin Koyon Tauhidi ta Baptist - 180
16) Jami'ar Anchor, Ayobo - 180
17) Jami'ar Kiwon Lafiya ta Pamo - 180
18) Jami'ar Redeemers - 180
19) Jami'ar Landmark - 180
20) Jami'ar Tarayya ta Alex Ekwueme - 180
21) Jami'ar Ilorin - 180
22) Jami'ar Jos - 180
23) Jami'o'in Tarayya (Federal Universities) - 180
24) Jami'ar Abuja - 180
25) Jami'ar Bayero, Kano -180
26) Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria - 180
27) Jami'ar Augustine - 180
28) Jami'ar Jihar Rivers - 180
29) Makarantar Koyon Tauhidi Ta Spiritan - 180
30) Adekunle Ajasin University - 180
31) Jami'ar Jihar Imo - 180
32) Makarantar Koyon Aikin Dan Sanda -180
33) Makarantar Falsafa ta Spiritan -180
34) Jami'ar Fatakwal – 180
35) Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola -180
36) Makarantar Koyon Falsafa ta Claretian -180
37) Makarantun Horas da Dakarun, NDA, Kaduna - 180
38) Jami'ar Jihar Binuwe -180
39) Makarantar Koyon Kwarewa a Limancin Addinin Kirista ta Majalisin Hikima -180
40) Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Ondo - 180
41) Jami'ar Olabisi Onabanjo - 180
42) Jami'ar Tarayya ta Noma - 180
43) Jami'ar Kiwon Lafiya ta Bayelsa - 180
44) Jami'ar Tarayya ta Fasaha, Imo - 180
45) Jami'ar Tarayya ta Fasaha, Akure - 180
46) Jami'ar Najeriya, Nsuka -180
47) Jami'ar Tarayya ta Albarkatun Man Fetur - 180
48) Jami'ar Kiwon Lafiya ta Jihar Ondo - 180
49) Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa- 180
50) Jami'ar Uyo -180
51) Jami'ar Ambrose Alli - 180
Akwai makarantu masu bayar da shaidar digiri 182 a Najeriya, 10 daga cikinsu sun kayyade 200 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karantunsu, sai kuma 11 sun takaita a kan maki 190 zuwa sama.
Kimanin jami'o'i 51 sun kayyade 180 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatu.
Makarantu 64 sun takaita a kan maki 170 zuwa sama, sai kuma 112 da suka riki 160 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatu, yayin da 69 suka takaita a kan 160 ko kasa da haka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng