Yadda cutar coronavirus ta hallaka matashin dalibi dan Najeriya da ke karatu a Amurka

Yadda cutar coronavirus ta hallaka matashin dalibi dan Najeriya da ke karatu a Amurka

Bassey Offiong dalibi ne dan asalin Najeriya ne da ke karatu a jami'ar yammacin Michigan da ke Amurka, amma cutar coronavirus ce tayi ajalinsa.

Dan shekaru 25 din ya mutu ne a ranar Asabar din da ta gabata. Zai kammala karatunsa ne nan da makonni kadan.

Kamar yadda jaridar Detroit News ta bayyana, Asari Offiong 'yar uwar mamacin ce kuma dan uwan nata, kafin ya mutu, ya sanar da ita cewa yana fama da zazzabi, kasala da tsinkewar numfashi, wadanda alamu ne na cutar coronavirus.

Ta ce dan uwanta ya sanar da ita cewa an ki yi mishi gwajin cutar wanda ake yi a yankin Kalamazoo.

Yadda cutar coronavirus ta hallaka matashin dalibi dan Najeriya da ke karatu a Amurka

Kwayar cutar coronavirus
Source: UGC

"Na fada masa cewa ya je a yi masa gwajin cutar covid-19, amma sai yace min ya je amma sun ki yi masa gwajin," a cewarta.

Duk da ta ki bayyana sunan asibitin da aka ki yi wa Bassey gwajin, ta ce wani ma'aikacin kiwon lafiya ya tabbatar mishi da cewa yana da cutar numfashin.

Ta kara da cewa dan uwanta bashi da cutar kafin nan. "Na san Ubangiji ya karbi bakuncinsa a lahira don ya fi mu son shi," a cewar Offiong.

DUBA WANNAN: An sallami mutane biyar da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya

An kwantar da Bassey a asibitin Beaumont da ke Royal Oak kuma yayi makon shi na karshe da taimakon na'urar numfashi.

A takardar da Edward Montgomery ta jami'ar yammacin Michigan ta fitar, shugaban makarantar ya ce Bassey mutum ne mai tsananin kwazo.

"A madadin daukacin jama'ar Bronco, ina mika sakon ta'aziyyata ga 'yan uwansa da suka hada da 'yar uwar shi Asari, wacce ta dinga sanar damu halin da yake ciki akai-akai," a cewarsa.

A ranar Juma'a ne hukumar makarantar ta bayyana cewa dalibai uku sun kamu da muguwar cutar coronavirus din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel