Mutanen gari sun tsere daga gidajensu a yayinda Boko Haram ta kai hari a kauyen Borno
- Jama'a mazauna kauyen Womdeo da ke Askira Uba suna tsaka mai wuya
- Mayakan ta'addanci na Boko Haram a halin yanzu suna cin karensu babu babbaka a kauyen
- Sakamakon musayar wuta da ake yi da mayakan, soji 6 da farar hula 1 sun mutu
Daruruwan farar hula a halin yanzu suna gudun ceton rai tare da neman mafaka sakamakon sabon hari da ake zargin mayakan ta'addanci na Boko Haram suke kaiwa karamar hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno.
An gano cewa miyagun a halin yanzu suna ta bankawa gidaje da ke kauyen Womdeo wuta da ke karamar hukumar Askira Uba ta Jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter
Kamar yadda daya daga cikin mazauna yankin da ke gudun ceton rai, Musa Ishaiku ya ce, "daruruwan mazauna garin a halin yanzu suna cikin daji inda suka boye cike da tsoro tare da tunanin inda sauran 'yan uwansu suke."
"Sun iso wurin karfe 6:30 na yamma kuma sun fara harbi ta ko ina. Jama'a sun gigice sakamakon wasu iyayen da suka kasa ganin 'ya'yansu. Suna kallon yadda ake kone gidajensu."
Wani mazaunin yankin mai suna Steve Mamza ya ce mayakan ta'addancin sun iso garin da yawansu.
KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau
"A halin yanzu da nake muku magana suna cikin kauyen Womdeo kuma sun fi sa'o'i biyu a ciki. Da yawan mutanenmu suna neman mafaka," Mamza yace.
A lokacin rubuta wannan rahoton, rundunar sojin Najeriya bata tabbatar da aukuwar lamarin ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mayakan ta'addancin sun kai hari mazaunin sojin Najeriya da ke Kusa kusa da garin Chibok wurin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin.
A halin yanzu, sojoji shida da wani farar hula ya rasa ransa yayin musayar wuta da suke yi.
A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.
A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng