Akwai yiwuwar kudin shan wuta ya karu a Ranar 1 ga Watan Afrilu

Akwai yiwuwar kudin shan wuta ya karu a Ranar 1 ga Watan Afrilu

Daga Ranar 1 ga Watan Afrilun 2020, ‘Yan Najeriya za su gamu da karin kudin wutar lantarki kamar yadda mu ka samu labari daga wata majiya mai karfi.

A shekarar bara watau 2019 ne Hukumar NERC mai lura da sha’anin wutar lantarki ta bayyana cewa za a kara kudin wutar lantarki a farkon Watan Afrilu.

Hukumar NERC ta kasa ta yi wasu ‘yan sauye-sauye a sha’anin kudin wuta. Wanda wannan ya sa dole farashin da mutane ke biya domin samun lantarki ya karu.

Majiyar ta bayyana cewa hukumar NERC ba ta niyyar ja da baya a wannan shiri da ta ke yi na kara kudin wutan lantarki duk da cewa an shiga mawuyacin hali.

A halin yanzu ana fama da annobar COVID-19 a Najeriya da wasu kasashen Duniya. Wannan ya sa wasu su ka fara kiran a dakatar da biyan kudin wuta da ruwa.

KU KARANTA: Kudin yin waya da aika sako da hawa yanar gizo zai karu

Akwai yiwuwar kudin shan wuta ya karu a Ranar 1 ga Watan Afrilu
Ministan wutan lantarkin Najeriya Injiniya Saleh Mamman
Asali: Facebook

Wani ma’aikacin kamfanin raba wutar lantarki ya shaidawa ‘Yan jarida cewa hukumar NERC ba ta aiko masu da takarda ta na neman a dakatar da karin kudin ba.

Idan har abubuwa su ka tafi a haka, babu abin da zai hana daga gobe Ranar Laraba watau 1 ga Watan Afrilun 2020, jama’a su wayi gari da sabon farashin wuta

Jaridar ta yi yunkurin tuntubar Mai magana da yawun bakin NERC, Usman Arabi domin jin matsayar hukumar game da wannan kari da ake hari a Afrilu.

Arabi ya bayyana cewa ya tafi wani kwas don haka bai san maganar ba. Jami’in da ya ke rike da wannan kujera a daidai wannan lokaci bai iya cewa uffan ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng