Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter

Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter

- Wata mata ta wallafa hotunan mahaifiyarta a dandalin sada zumunta na Twitter don nema mata miji

- Matar ta bayyana cewa tsohon mijin mahaifiyarta ya sake ta ya koma kauye don cigaba da rayuwa da wata matar

- Ta ce shekarun mahaifiyarta 60 don haka duk wani mutumin kirki da shekarunsa suka kai 65 yana iya neman auren

Wata ma'abociyar amfani da shafin dandalin sada zumunta na Twitter @Halimalfade ta fara nema wa mahaifiyarta mai shekaru 60 da 'yan kai mijin aure.

Ta bayyana cewa tsohon mijin mahaifiyarta ya sake ta ya koma kauye domin ya cigaba da rayuwa da wata sabuwar matan.

Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter
Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter. Hoto: @Halimalfade
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)

Budurwar mai @Halimalfade wadda ta wallafa hoton mahaifiyarta a Twitter ta rubuta cewa;

"Ina nema wa mahaifiyata abokin zama. Mijinta baya nan da izinin Allah. Mutum mai karamci, fara'a, ban dariya kuma mai bukatan abokin zama. Dattijuwa ce tana da jikoki kuma shekarunta sun haura 60 don haka duk wanda shekarunsu suka haura 65 ya yi. Tana da fuskar kuriciya kuma mace ce mai nagarta, kyau da kuma ba cima zaune bane"

KU KARANTA: 'Yan sanda sun hana yin casun badala a Adamawa

Wannan rubutun ya janyo hankulan mutane da dama a dandalin na Twitter.

@cchukudebelu ya ce:

"A yi min afuwa. Ko muna iya ganinta ba tare da ta shafa kayan kwalliya ba?

@Halimalfade ta amsa

"Ban yi tsammanin ina da wani hoton ba amma ga wani nan shima sabo ne.

Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter
Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter. Hoto: @Halimalfade
Asali: Twitter

@Somidotun7 ya ce:

Mene kike nufi da ce mijinta baya nan insha Allah?

@Halimalfade ta amsa:

Mutumin ya sake ta ya koma kauye da zama domin ya cigaba da rayuwarsa da wata matan Masha Allah.

@Tessammm ya ce:

Ni kam sai dai in ce masha Allah. Mutumin dama ba alheri bane. Ina mata addu'ar samun wani mai sonta na kirki.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: