Matata na barazanar kashe ni, Miji ya fadawa kotu

Matata na barazanar kashe ni, Miji ya fadawa kotu

- Wani magidanci Kazeem Adebiyi ya tafi kotu yana rokon ta raba auren sa da matarsa Rukayat bisa zargin yunkurin kashe shi

- Adebiyi ya bayyana cewa watan sa hudu a boye inda bata sani ba saboda tayi alwashin kashe shi in dai ta ganshi

- Alkalin kotun Henry Agbaje ya raba auren tare da mika alhakin kula da yaran a hannun matar

Wani ma'aikacin kamfani, Kazeem Adebiyi, ya shaida wa wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ile-Tuntun ta raba auren sa mai shekara uku da matar sa, Rukayat bisa zargin yunkurin kashe shi da ke yawan yi da zarar sun dan samu sabani.

Da ya ke zartar da hukunci, shugaban kotun, Cif Henry Agbaje, ya raba auren, a cewar sa a samu kwanciyar hankali tsakanin Adebiyi da Rukayat.

Agbaje ya kuma mika alhakin kula da yaran su biyu a hannun Rukayat tare da umartar Adebiyi da ya dinga biyan N8,000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa, tare da daukar nauyin karatunsu da duk wata dawainiya.

Mata ta na barazanar kashe ni - Miji
Matata na barazanar kashe ni - Miji. Hoto: @daily_trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter

Tun da fari, Kazeem ya ce ya bar gidan sa saboda matarsa ta haramta masa gidan ta hanyar musguna masa da kuma tsoratar da rayuwarsa.

Ya ce duk sanda muka samu sabani da Rukayat sai ta yaga min kaya sun zama tsumma.

"Ba abin da zanyi na burge Rukayat da zai sa ta zauna dani lafiya, ta zame min shedaniya.

"A wata hudun da suka gabata, na zama dan gudun hijira a inda bata sani ba, saboda ta yi alwashin kashe ni duk inda ta ganni.

"Har yunkurin kashe ni tayi kafin na samu na gudu, kuma da gaya wa mahaifiyarta halin da ake ciki, ita ta ce na tafi kotu in bazan iya ba.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

"Na yi duk abin da zan iya don biya wa Rukayat bukatun ta, har jarin ₦100,000 na bata don ta fara kasuwanci, amma ta kashe.

"Da naki bata wasu kudin sai ta fara barazanar kashe ni," inji Kazeem.

Sai dai, Rukayat ta kalubalanci karar, amma ta kasa karyata da yawa daga cikin zargin da aka yi akan ta.

Sai dai ta ce yaran ta har yanzu kanana ne kuma zasu sha wahala idan baban su ya rabu da ita.

"Adebiyi bai san hakkokin aure ba;ko tausaya wa ni da yara baya yi," a cewar ta.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel