Bincike ya nuna yan Najeriya sun fi damuwa da rashin tsaro da talauci fiye da korona
- Yan Najeriya da dama basu damu da mummunan annobar nan ta korona ba
- A bisa ga wani bincike, mutane sun damu da talauci, rashin tsaro da sauransu
- Cibiyar bincike da tuntuba ta Infotrak ce ta gudanar da bincike don shekarar 2021
Wani bincike ya nuna cewa yan Najeriya sun fi damuwa da wasu abubuwa biyar fiye da mugunyar annobar korona wacce ta kashe fiye da mutane 1,300 a watanni tara da suka gabata.
Binciken da cibiyar bincike da tuntuba ta Infotrak ce ta bayyana hakan a wani bincike da ta gudanar.
A cewar binciken, kaso bakwai cikin dari ne kacal ke nuna damuwa a kan annobar COVID-19 fiye da sauran lamura a 2021.
KU KARANTA KUMA: 2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbaj-Zulum tikiti
A bisa ga binciken, ga abubuwan da yan Najeriya suka fi nuna damuwa a kai a shekarar 2021:
1. Rashin tsaro
2. Rashin aikin yi
3. Talauci
4. Rashawa
5. Tsadar rayuwa
KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta
Jaridar Punch ta nuna cewa kaso 16 cikin dari na binciken sun fi damuwa da rashin tsaro da laifika a 2020, yayinda kaso 14 cikin dari suka fi damuwa da rashin aikin yi.
A wani labari na daban, mun ji cewa wani asibiti a Warsaw yana cikin tashin hankali saboda yin allurar rigakafin COVID-19 ga mashahurai da 'yan siyasa, wanda ya haifar da fushin jama'a kuma ya haifar da binciken gwamnati wanda ya fara a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.
Poland, wacce kamar yawancin kasashen Turai ta fara aikin rigakafin ta ne a ranar 27 ga Disamba, wanda ya kamata ta yiwa ma'aikatan lafiya allurar rigakafin ne a karkashin shirin gwamnati.
Amma asibitin likitanci na Warsaw a makon da ya gabata ya ce ya kuma yi wa wasu mutane 18 rigakafin wadanda ake son su yi aiki a matsayin jakadu na kamfen din yada rigakafin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng