Baya da Maiduguri, babu inda ke da tsaro a cikin jihar Borno, Farfesa Dikwa

Baya da Maiduguri, babu inda ke da tsaro a cikin jihar Borno, Farfesa Dikwa

- Mamba a kungiyar dattawan Borno, Farfesa Khalifa Dikwa ya koka a kan tsanantar rashin tsaro a Borno

- Ya tabbatar da cewa babu wani gari a jihar baya da Maiduguri da ke da tsaro a dukkan jihar Borno

- Ya koka da rashin jin shawarar soji a yayin da suka kwato wasu garuruwa a 2014, hakan ne ya kawo abinda jihar ke ciki yanzu

Farfesa Khalifa Dikwa, daya daga cikin dattawa a kungiyar dattawan Borno ya nuna damuwarsa a kan hauhawar rashin tsaro a yankin.

Ya ce baya da babban birnin jihar Borno, babu inda mutane ke rayuwa da tsaro a fadin jihar.

"Ko da a ce babu Boko Haram a wasu wurare, sun riga sun tsorata jama'a kuma suna zukatan jama'a tare da hana su zaman lafiya," Dikwa ya sanar da Channels TV a wani shirin daren ranar Litinin.

"Lokaci zuwa lokaci suke shigowa a baburansu su zo suna hantarar jama'a har su biya haraji. Suna kai hari a kowanne lokaci."

KU KARANTA: Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC

Baya da Maiduguri, babu inda ke da tsaro a cikin jihar Borno, Farfesa Dikwa
Baya da Maiduguri, babu inda ke da tsaro a cikin jihar Borno, Farfesa Dikwa. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

Ya yi ikirarin cewa dakarun sojin Najeriya basu ji shawarar da aka basu ta zama a dukkan iyakokin tudu na kasar nan bayan sun tarwatsa Boko Haram a 2014.

"A lokacin, PMC ta ce toh mun yi iyakar kokarinmu sauran ya rage na siyasa ne. Ku tattauna da 'yan ta'adda domin kara samun karfin tsaro," Malamin jami'ar yace.

"Kuma ku bar sauran jami'an tsaro su mamaye inda kuka kwace. Ku bar sojoji su tsaya a iyakokin tudu na kasarku."

Farfesa Dikwa wanda ya bukaci jami'an tsaro su hada kansu wurin yakar ta'addanci, ya ce dakarun soji kadai ba za su iya yakar ta'addanci ba a jihar Borno.

KU KARANTA: Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Asabar ya ziyarci mafarauta shida da a halin yanzu suke karbar kulawar masana kiwon lafiya a asibitin koyarwa da ke Maiduguri.

Mafarautan sun samu miyagun raunika sakamakon dashen abu mai fashewa da mayakan Boko Haram suka yi wanda ya tashi da mafarautan yayin da suke sintiri a dajin Sambisa.

Kusan mafarauta bakwai ne a take suka mutu yayin da wasu 16 suka samu miyagun raunika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel