Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kaiwa mafarautan da ke asibiti ziyara

- An gano cewa wani abu mai fashewa ya tashi da mafarautan yayin da suke sintiri a Sambisa

- A take 7 daga cikinsu suka mutu yayin da 16 daga cikin suka samu miyagun raunikan da ya kaisu asibiti

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Asabar ya ziyarci mafarauta shida da a halin yanzu suke karbar kulawar masana kiwon lafiya a asibitin koyarwa da ke Maiduguri.

Mafarautan sun samu miyagun raunika sakamakon dashen abu mai fashewa da mayakan Boko Haram suka yi wanda ya tashi da mafarautan yayin da suke sintiri a dajin Sambisa.

Kusan mafarauta bakwai ne a take suka mutu yayin da wasu 16 suka samu miyagun raunika.

Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna
Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna. Hoto daga @GovBorno
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mafarautan suna kan sintiri ne bayan samun rahoton cewa mayakan Boko Haram sun sace wasu shanu a kauyen da ke kusa.

Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna
Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna. Hoto daga @GovBorno
Source: Twitter

Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna
Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna. Hoto daga @GovBorno
Source: Twitter

Kwamishinan wasanni na jihar, Sainna Buba ya ce daga cikin 16 da ke asibiti, an sallama 11 bayan samun taimakon likitoci.

Zulum ya sauka a Maiduguri a ranar Asabar bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da darakta janar na NEMA, Air Vice Marshal Muhammadu Muhammad mai ritaya.

KU KARANTA: Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin

Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna
Zulum ya yi muhimmiyar ganawa da ministan jin kai, ga abinda suka tattauna. Hoto daga @GovBorno
Source: Twitter

KU KARANTA: 2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga

A wani labari na daban, mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace 'yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel