Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta

Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta

-Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta ga masu shigowa daga kasashen duniya

- Kasar ta bayyana cewa wasu maso shigowa sai sun debe kwanaki hudu a killace kafin shiga kasar

- Kasar ta bayyana samun saukin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar

Saudiyya a ranar Lahadi ta sanar da sake bude kan iyakoki da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa bayan dakatarwar da aka yi ta makwanni biyu da nufin dakile yaduwar wata sabuwar cutar ta Covid-19.

Gwamnatin ta ba da umarnin a dauke "matakan kariya da suka shafi yaduwar wani sabon nau'in kwayar cutar corona," in ji ma'aikatar cikin gidan, a cewar kamfanin dillancin labarai na Saudi Arabia.

Saudi Arabiya ta bayyana samun sama da mutane 363,000 da suka kamu da cutar, ciki har da sama da mutane 6,200 da suka mutu - mafi girma a tsakanin kasashen larabawan Tekun Fasha - amma kuma ta bayar da rahoton yawan samun sauki.

Riyadh ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa da kuma isa ta mashigar kasa da mashigai a ranar 21 ga Disamba.

KU KARANTA: Boko Haram sun sace ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta
Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta Hoto: Facebook/Arab News
Asali: Facebook

Sauran kasashen yankin Gulf, Oman da Kuwait, wadanda suka dauki irin wannan matakin, suma sun dauke su a kwanakin baya.

Amma matafiyan da suka dawo daga Biritaniya, Afirka ta Kudu ko “duk wata ƙasa da sabon nau'in kwayar cutar ta coronavirus ke yaɗuwa” za su fuskanci ƙarin takunkumi, in ji sanarwar.

Baƙi da ke zuwa daga waɗannan ƙasashen dole ne su kwashe kwanaki 14 a wata ƙasa kafin su shiga Saudi Arabiya, kuma su nuna gwajin cewa ba sa dauke da cutar.

'Yan kasar ta Saudiyya da suka dawo daga wadannan kasashen za su iya shiga kai tsaye - amma dole ne su kwashe makonni biyu a keɓe lokacin isowa, kuma za a yi musu gwaji.

KU KARANTA: Kasafin kudi: Sanwo Olu ya sa hannu, Gwamnatin Legas za ta kashe N1.163tr

A watan da ya gabata Saudi Arabiya na daga cikin kasashen Gulf na farko da suka fara wani gagarumin aikin riga-kafi ta amfani da jab din Pfizer-BioNTech.

A wani labarin, A ƙalla sama da fararan hula 70 ne aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu dake ƙasar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali.

Kimanin mutum 50 ne aka kashe a ƙauyen Tchombangou sannan 17 suka ji mummunan rauni kamar yadda wani jami'in tsaro ya tabbarwa Reuters ya kuma nemi da a sakaye sunansa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Wata majiya daga wani jami'in harkokin cikin gida na ƙasar ta Nijar da shima ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da an kashe sama da kimanin mutum 30 a Zaroumdareye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel