Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna

Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna

- Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon sunan zolaya

- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana PDP a matsayin jami'ar karya

- Garba Shehu ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta fadi zaben 2015 saboda cin hanci

A ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu, ne fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta bayar da kwangilolin bogi, na karya, domin kawai a wawure kudaden jama'a, lamarin da a karshe ya kassara tattalin arzikin kasa.

KARANTA: 'Yan bindiga sun harbe wani limami a Kaduna saboda yawan sukarsu a hudubarsa

Garba Shehu ya bayyana cewa 'yan Nigeria zasu sake juyawa PDP baya yayin zaben shekarar 2023 saboda sun gano cewa jam'iyyar babu abinda ta kunsa sai karya.

Wani bangare na jawabin ya bayyana cewa; "cin hanci ne ya jawowa jam'iyyar PDP faduwa zabe a shekarar 2015.

Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna
Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna Hoto (@Grabashehu, @OfficialPDP)
Asali: Twitter

"Ita kuwa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta tsare kima mutuncinta. Ta samu nasarar murkushe cin hanci a fadar shugaban kasa.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

"A yanzu babu Mai kiran gwamnan banban bankin kasa (CBN) daga fadar shugaban kasa domin bashi umarnin ya kawo madarar kudi a takardun Naira, Dollar, Pounds, Euro, ko Renminbi".

Jawabin ya bayyana cewa tasirin jam'iyyar PDP ya kare, mutuncinta tuni ya zube, Kuma 'yan Nigeria ba zasu manta da irin ta'asara da suka tafka ba yayin mulkinsu.

A jihar Kano, jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023, kamar yadda rahotanni suka rawaito.

Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba.

Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng