Boko Haram sun tsallaka Nijar, sun kashe mutane fiye da 70

Boko Haram sun tsallaka Nijar, sun kashe mutane fiye da 70

- Wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun tsallaka jamhuriyar Nijar tare da kashe mutane fiye da 70

- An kai harin ne a wasu kauyuka guda biyu da ke daura da iyakar kasar Nijar da Mali

- Kasashen nahiyar Afrika na fama da hare-haren 'yan ta'dda da suka hada da Boko Haram, ISWAP, da 'yan bindiga

A ƙalla sama da fararan hula 70 ne aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu dake ƙasar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali.

Kimanin mutum 50 ne aka kashe a ƙauyen Tchombangou sannan 17 suka ji mummunan rauni kamar yadda wani jami'in tsaro ya tabbarwa Reuters ya kuma nemi da a sakaye sunansa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Wata majiya daga wani jami'in harkokin cikin gida na ƙasar ta Nijar da shima ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da an kashe sama da kimanin mutum 30 a Zaroumdareye.

KARANTA: Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

Da jin faruwar wannan kazamin al'amari ne, gidan jarida na Reuters ya yi kokarin jin ta bakin manyan jami'an da alhakin hakan ya shafa na ƙasar amma haƙansu ba ta vimma ruwa ba.

Boko Haram sun tsallaka Nijar, sun kashe mutane fiye da 70
Boko Haram sun tsallaka Nijar, sun kashe mutane fiye da 70
Asali: Twitter

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

Afrika ta yamma dai na fama da da hare-haren taaddanci daga dakarun kungiyoyi da suke da alaƙa da kungiyar alQaeda. Daga iyakokin yamma, hare-haren kuma ya fi kamari a yankunan Mali, Burkina Faso, sai kuma kudu maso gabas inda hare-haren ya kazanta a yankunan Nijar da Najeriya.

Legit.ng ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana salon da ta bi na ceto yaran makarantar sakandire ta kimiyya dake ƙanƙara su 344 waɗanda yan ta'adda suka sace ranar 11 ga Disamba, 2020.

Kazalika, ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban.

A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun 'yan ta'addar, kamar yadda Punch ta rawaito.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng