Mayakan Boko Haram sun sace mata 4 a Adamawa

Mayakan Boko Haram sun sace mata 4 a Adamawa

- Jama'ar karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa sun koka a kan harin da Boko Haram ke kai musu

- A cikin kwanakin nan, mayakan ta'addancin da ke zama a dajikan yankin sun sace masu mata hudu

- Sun sako daya daga cikin matan ganin matar aure ce kuma a cewarsu ta yi musu tsufa don haka bata da abun mora

Mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace 'yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu.

Mayakan Boko Haram sun sace mata 4 a Adamawa
Mayakan Boko Haram sun sace mata 4 a Adamawa. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari

Daga bisani sun saki matar auren saboda sun ce ta yi musu tsufa.

"Har yanzu 'yan matanmu na hannunsu tun sace su da suka yi a makon da ya gabata. Muna kira ga gwamnati da dakarun soji da su yi duk abinda ya dace wurin ceto su," wani mazaunin yankin ya sanar.

Wani mazaunin yankin har ila yau mai suna Iskarju Ezekiel ya yi kira ga hukumomin tsaro da su taimaka wurin kakkabo 'yan Boko Haram da ke da maboya a kewayen Madagali da sauran yankunan Borno.

"Abubuwan na faruwa kadan-kadan saboda akwai ragowar 'yan Boko Haram a dajikan da ke zagaye da mu. Muna rayuwa cikin tsoro ballantana da suka sace 'yan mata a ranar Litinin," yace.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo

A wani labari na daban, Jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan.

Ya ce shugaan kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.

Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel