Bidiyon mayakan ISWAP suna kashe wasu 'yan Najeriya 5 ya gigita jama'a
- Shahararriyar kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta saki wani bidiyo wanda ya firgita jama'a
- A bidiyon, an ga yadda mayakan suka halaka wasu mutum 5 'yan Najeriya da suka sace
- Sun ce hakan ramuwa ce ga Kiristoci na Najeriya da na sauran duniya baki daya
Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana bidiyon yadda ta halaka wasu Kiristoci da ta cafke a cikin kwanakin nan a arewa maso gabas na kasar nan.
Bidiyon ya fita a ranar Talata a sa'ar da bangaren Shekau na Boko Haram suka halaka wasu mafarauta 7 a Borno sannan suka raunata wasu 19.
A bidiyon mai tsayin dakika 49, an ga 'yan ta'addan inda suka rufe fuska a tsaye dauke da bindigogi da kuma wasu mutane gurfane a gabansu.
KU KARANTA: Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari
Kamar yadda aka ji daya na sanarwa, za su kashe mutane biyar din ne a matsayin ramuwa da kuma aike sako ga Kiristocin Najeriya da na duniya gaba daya.
Kammala jawabin ke da wuya suka bindigesu ta keya.
KU KARANTA: Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)
A wani labari na daban, an kashe shugaban kungiyar mafarauta na jihar Adamawa, Young Mori, a wata musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda iyalansa da wasu majiyoyi suka tabbatar.
Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyata don kokarin yaki da 'yan ta'adda a jihohin arewa. Shugaban kungiyar, Salihu Wobkenso, ya tabbatar da faruwar lamarin. A cewarsa, an kashe Mori ne a Kaduna.
"Wannan mummunan labari ne ga mafarautanmu. Young Mori, daya daga cikin jaruman mafarautan jihar Adamawa daga karamar hukumar Guyuk ya riski ajalinsa a jihar Kaduna. Masu kiwon shanu sun kashe shi da safiyar yau."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng