2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

- Kafin zuwan zaben shugaban kasa na 2023, Afenifere ta yi magana a kan yadda ta shirya goyon bayan 'yan takara

- Kungiyar Yarbawan ta ce tana tsayawa dan takara ne idan ta duba abinda ya bayyana ba jam'iyyarsa ba

- Da aka tambayeta ko za ta goyi bayan Jonathan a 2023, ta ce za ta duba abubuwan da ya kamata kafin ta yanke matsayarta

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta ce bata taba shiga cikin wani halin tsoro ba matukar ta zo goyon bayan dan takara ballantana idan ra'ayinsa ya zo daidai da nata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kakakin kungiyar, Yinka Odumakin ya sanar da hakan a ranar Laraba, 30 ga watan Disamba a yayin da aka tambayesa ko za su goyi bayan Goodluck Jonathan a 2023 idan ya fito takara.

KU KARANTA: Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi da safarar yara

2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara
2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara. Hoto daga Goodluck Jonathan, Save Nigeria Group
Asali: Facebook

A kalamansa: "Kamar yadda nace, idan lokacin ya zo zamu duba dukkan abubuwan da suka dace kafin mu samu matsaya. Afenifere bata tsoron bayyana matsayarta kuma za mu bada dalilan da suka sa muka sakankance cewa dan takaran ya fi inganci."

Kungiyar ta kara da bayyana dalilan da yasa ta goyi bayan jam'iyyar PDP a zabukan 2015 da 2019.

Ta ce sun yi hakan ne saboda 'yan takarar jam'iyyar PDP sun yi alkawarin kawo tsarin gyara a kasar idan sun yi nasara.

KU KARANTA: Hotunan ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a kan hanyar Kaduna

A wani labari na daban, an kashe shugaban kungiyar mafarauta na jihar Adamawa, Young Mori, a wata musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda iyalansa da wasu majiyoyi suka tabbatar.

Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyata don kokarin yaki da 'yan ta'adda a jihohin arewa. Shugaban kungiyar, Salihu Wobkenso, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, an kashe Mori ne a Kaduna. "Wannan mummunan labari ne ga mafarautanmu. Young Mori, daya daga cikin jaruman mafarautan jihar Adamawa daga karamar hukumar Guyuk ya riski ajalinsa a jihar Kaduna. Masu kiwon shanu sun kashe shi da safiyar yau."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel