Gwamnatin Najeriya za ta ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa

Gwamnatin Najeriya za ta ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa

- Hukumomin Najeriya ta tattauna da na Saudiyya kan batun wani dan Najeriya da ke tsare a kasar shekaru 18

- Kasar Saudiyya ce ta zartarwa da Sulaimon Olufemi hukuncin kisa bayan an same shi da laifin kashe dan sanda

- Yanzu haka za a iya yafewa Sulaiman kadai idan yar jami'in mai shekara 20 da ya kashe ta amince

Shugaban hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce gwamnatin Najeriya tana duba lamarin Sulaimon Olufemi wanda kasar Saudiyya ta yankewa hukuncin kisa bisa zargin kashe jami'in dan sanda.

Shugaban NiDCOM ya bayyana haka a wata tattaunawa da iyalan Olufemi wanda suke rokon hukumomin Saudiyya su sakar musu dansu, The Punch ta ruwaito.

Gwamnatin Najeriya zata ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yankewa hukuncin kisa
Gwamnatin Najeriya zata ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yankewa hukuncin kisa. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

Ta ce NiDCOM tana aiki da hukumomin Najeriya da ke Kasar Saudi Arabia, ta kara da cewa ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, yana tattaunawa da hukumomin Saudiyya dangane da batun.

Kuma shugaban kwamitin harkokin waje, Akande Sadipe ya ce.

KU KARANTA: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

Yancin Olufemi yana hannun yar dan sandan da ya kashe kuma shekarar ta biyu lokacin. Idan ta yafe masa yanzu tana da shekara 20 zai shaki iskar yanci.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel