Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande

Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande

- Alhaji Yahaya Kwande ya magantu a kan matsalar rashin tsaro a kasar

- Jigon na kungiyar dattawan arewa ya ce gazawar gwamnatin Buhari ne musabbabin rashin tsaro a Najeriya

- Ya yi kira ga gwamnati da ta jingine duk wasu ayyukanta ta mayar da hankali wajen inganta al’amuran da suka shafi tsare rayuka da dukiyoyin al’umma

Wani mamba a kungiyar dattawan arewa, Alhaji Yahaya Kwande, ya alakanta matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da shi da gazawar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fashi da makami da sace-sacen mutane ya yiwa kauyuka da dama a kasar katutu a baya-bayan nan inda aka kasha wasu da dama.

Kwande, wanda ya zanta da jaridar Daily Trust a Jos ya ce: “gwamnati ta gaza kuma kasar ta kare. Yan bindiga da masu garkuwa na kashe mutane.

Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande
Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande Hoto: @NigerianTribune
Asali: Twitter

"Tsaro a kasar ya tabarbare. Allah kadai ya san abunda ke faruwa a kauyukan kasar nan. Muna cikin tsananin tsoro.”

KU KARANTA KUMA: 2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

Ya ce mutanen birni da na kauye a kasar basu da wani sukuni, inda yace hatta baki sun zama barazana ga mutane a gidajensu kuma babu wajen guduwa.

Kwande ya ce rashin baiwa tsaro muhimmanci da Gwamnatin Buhari ta yi tun da farko ya yi tasiri wajen jefa kasar cikin halin da ta tsinci kanta a yanzu.

Ya kara da cewa, rashin jajircewa da halin ko in kula da gwamnatin ta nuna gami da kwadayi da son zuciya, sun taka rawar gani wajen bai wa matsalar tsaro gudunmuwa mai girman gaske a kasar.

Ya kuma tunantar da gwamnatin cewa mutane take mulka ba dabbobi ba, inda yayi kira da a yi wa harkar tsaro karatun ta nutsu.

Ya kuma nemi gwamnati ta jingine duk wasu ayyukanta ta mayar da hankali wajen inganta al’amuran da suka shafi tsare rayuka da dukiyoyin al’umma wanda shi ne nauyi na farko da rataya a wuyanta.

KU KARANTA KUMA: 2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa

Sai dai ya ce har yanzu ana iya samun aminci a kasar amma sai gwamnati ta koma kan taswirarta ta tsare-tsare domin ganin abin da zai faranta wa jamai’an tsaro.

Ya kuma ce dole ne ta hada kai da ’yan adawarta domin tabbatar da zaman lafiya don don gwamnati kadai ba za ta iya wannan aiki ba.

A wani labarin, majalisar Kansiloli ta tsige Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Kwamred Dauda Suleiman Chukuba, bisa zargin Almundahana.

A cewar majalisar, sun bawa shugaban duk wata dama domin ya kawar kansa daga zargin da ake yi masa amma sai ya nuna musu raini.

Ana zargin Kwamred Chukuba da yin almubazzaranci da barnatar da kudaden shiga da karamar hukuma ta samu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng