Kada wani abu ya samu Bishop Kukah, Inji Apostle Suleman

Kada wani abu ya samu Bishop Kukah, Inji Apostle Suleman

- Ya zama dole a bayar da tabbaci da mutunta tsaron Mathew Kukah, a cewar Apostle Suleman

- Faston ya ce mutane su kyale limamin cocin na Katolika sannan su mayar da hankali kan yaki da rashin tsaro

- A cewarsa, Allah zai mayar da martani ga duk wanda ke shirin taba dansa

Apostle Johnson Suleman, babban fasto kuma Shugaban cocin Omega Fire Ministries International, ya aika gagarumin gargadi ga wadanda ke sukar Bishop Mathew Kukah.

Limamin cocin ya bayyana cewa kada a kuskura ayi wani abu da zai illata limamin cocin na Katolika kan furucin da yayi a kan gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande

Kada wani abu ya samu Bishop Kukah, Inji Apostle Suleman
Kada wani abu ya samu Bishop Kukah, Inji Apostle Suleman Hoto: @APOSTLESULEMAN
Source: Facebook

Suleman ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa:

“Kada wani abu ya samu Bishop Kukah. Wadanda ke shirya hakan sun san abunda nake fadi. Kada mu tunzura abun ya kara girmama. Ku kyale mai suka da zuciya daya dannan ku magance yan ta’adda. Kada ku taba Bishop Kukah idan kuka taba ministocin Allah, Allah zai mayar maku da martani.”

KU KARANTA KUMA: 2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

A wani labari, Bishop na Katolika da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya fayyace biri har wutsiya kan cece-kucen da sakonsa na Kirsimeti ya haifar.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa babban faston ya ce shi bai yi kira ga juyin mulki ba a sukar da yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda aka rahoto, cewa kawai dai ya fadi ra’ayinsa ne bisa hujja.

Legit.ng ta tattaro cewa yayinda ya ke zargin Buhari da son kai a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, faston ya ce idan da ace Musulmin da ba dan arewa bane ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi masa juyin mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel