Kukah: Ban yi kira ga juyin mulki a kan gwamnatin Buhari ba, limamin Katolika ya fayyace gaskiya
- Bishop Kukah ya shawarci kafofin watsa labarai da su kawo rahoton labari yadda yake ba tare da kowani murdiya ba
- Kukah na martani ne ga sukar da ake masa kan sakonsa na Kirsimeti zuwa ga yan Najeriya
- Bishop ya bayyana cewa ra’ayin kansa kawai ya fada
Daga karshe Bishop na Katolika da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya fayyace biri har wutsiya kan cece-kucen da sakonsa na Kirsimeti ya haifar.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa babban faston ya ce shi bai yi kira ga juyin mulki ba a sukar da yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda aka rahoto, cewa kawai dai ya fadi ra’ayinsa ne bisa hujja.
Legit.ng ta tattaro cewa yayinda ya ke zargin Buhari da son kai a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, faston ya ce idan da ace Musulmin da ba dan arewa bane ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi masa juyin mulki.
Da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, Kukah ya ce babu adalci a rahoton cewa shi ya nemi ayi juyin mulki.
KU KARANTA KUMA: Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah
Ya ce:
“Babu adalci wani dan jarida ko wata kafar labarai ta ruwaito cewa na yi kira ga yin juyin mulki yayinda na bayyana ra’ayina game da Najeriya.”
Kan kira ga cewar ya ajiye limancinsa sannan ya shiga siyasa, malamin ya ce idan da zai shiga siyasa, toh da ya shige ta a zamanin marigayi Aminu Kano amma ba a yanzu ba.
Kukah ya kara da cewa shi baya shirin sanya kansa a siyasar bangaranci, cewa masu alakanta sakonsa da siyasar bangaranci na bin kidin ne.
Ya ce duk abun da ya fadi yana iya dadawa mutum ko ya bata masa, inda ya kara da cewa fadin nasa ra’ayin ba zai hana sauran mutane fadin nasu ra’ayin ba.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba
A wani labarin mun ji cewa kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta fito ta kare babban limaminta a Sokoto, Bishof Mathew Hassan Kukah.
Kungiyar ta CAN ta ce a jawabin da Mathew Hassan Kukah ya yi na bikin Kirismeti, babu inda ya soki Musulunci ko kuma ya yi kiran ayi juyin-mulki.
CAN ta zargi gwamnatin tarayya, shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da neman juya maganar da Faston ya yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng