Tsoron shugaba Buhari kuke yi, Shehu Sani ga 'yan majalisar wakilai

Tsoron shugaba Buhari kuke yi, Shehu Sani ga 'yan majalisar wakilai

- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki 'yan majalisar wakilai

- A cewar sanatan, 'yan majalisar suna tsoron Buhari ne shiyasa suka fasa gayyatarsa

- Ya ce ya kamata a ji ta bakin shugaban kasa musamman yadda ake yawan kai farmaki garuruwa

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce 'yan majalisar wakilai suna tsoron shugaba Muhammadu Buhari, shiyasa suka soke gayyatar da suka yi masa.

Sani ya yi wannan maganar ne da BBC Hausa, inda yace ya kamata shugaba Buhari ya bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

A cewarsa, babu dalilin da zai sanya a ce su gayyaci Buhari kuma su koma su canja ra'ayi.

Tsoron shugaban Buhari kuke yi, Shehu Sani ga 'yan majalisar wakilai
Tsoron shugaban Buhari kuke yi, Shehu Sani ga 'yan majalisar wakilai. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci

"Ana ta kashe mutane a kowacce rana, ana ta garkuwa da dubbannin jama'a dare da rana kuma alamu sun nuna cewa shugaban kasa bai damu ba. Wadannan suna cikin dalilan da suka sanya aka maka Jonathan da kasa.

"Menene amfanin fasa gayyatar shugaban kasa? Hakan yana nuna kuna tsoron shi ne. A kalla gayyatar za ta sanya shugaban kasa yayi wa 'yan Najeriya bayani su san matakan da yake kokarin dauka," yace.

KU KARANTA: Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda Janar Olu Bajowa mai ritaya ya ceci rayuwarsa inda ya tsallake mutuwa daga hannun Buka Suka Dimka a juyin mulkin 1976.

Obasanjo ya ce da Bajowa bai gayyacesa sunan dan sa ba, da tuni sojoji masu juyin mulki sun hallaka shi har lahira.

Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020 a jihar Ondo yayin bikin murnar cikar Bajowa shekaru 80 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng