Yadda aka kusa sheke ni har lahira, Obasanjo ya yi bayani

Yadda aka kusa sheke ni har lahira, Obasanjo ya yi bayani

- Olusegun Obasanjo ya yi magana a kan tsallake rijiya da baya da yayi a juyin mulkin 1976

- Tsohon shugaban kasan ya jinjinawa nagartar janar mai ritaya, Olu Bajowa

- Dattijon ya ce sojan mai ritaya ya kasance jajirtaccen soja da ya cece rayuwarsa

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda Janar Olu Bajowa mai ritaya ya ceci rayuwarsa inda ya tsallake mutuwa daga hannun Buka Suka Dimka a juyin mulkin 1976.

Obasanjo ya ce da Bajowa bai gayyacesa sunan dan sa ba, da tuni sojoji masu juyin mulki sun hallaka shi har lahira.

Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020 a jihar Ondo yayin bikin murnar cikar Bajowa shekaru 80 a duniya.

KU KARANTA: Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba

Yadda aka kusa sheke ni har lahira, Obasanjo ya yi bayani
Yadda aka kusa sheke ni har lahira, Obasanjo ya yi bayani. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Ya ce: "Ina da wani abu da zan fadi a kan Olu, kila ya sani ko kuma bai sani ba. A yayin da aka zo juyin mulkin Dimka, da ace Olu bai zama abinda yake ba da har da ni za a kashe.

"Bari in baku labari. Olu yana matukar girmama ni. Yana bin al'ada yadda ta dace. Ya haifa yaro namiji kuma yana son yi min takwara. Safiyar ranar da Dimka zai yi juyin mulki ya kira ni.

"Saboda haka na dinga jiran shi na tsawon lokaci bai zo ba har na saba lokacin da nake fita. Daga bisani yazo muka yi doguwar tattaunawa, hakan ce ta sa na yi lattin fita wanda hakan ya cece rayuwata."

KU KARANTA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna yadda yake da burin kawo karshen kalubalen da ke addabar arewa ta tsakiya a fannin tsaro.

A wasu hotunansa, an ga gwamnan jihar Kogin sanye da kayan sojoji inda ya tsinkayi dajin Irepeni da ke Kogi ta tsakiya domin ganawa da sojojin da ke dajin.

Wani Promise Emmanuel wanda ya bayyana kansa a matsayin babban sakataren yada labaran mataimakin gwamnan ya wallafa hotunan a Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel