Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi da safarar yara

Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi da safarar yara

- Mai rajin kare hakkin dan Adam, malam Lawal Gusau ya yi wa jaruma Nafisa Abdullahi fallasa

- Kamar yadda ya fitar a wata takarda, ya zargeta da fasa kwabrin miyagun kwayoyi tare da safarar yara

- Sai dai jarumar ta musanta hakan inda ta zargesa da zama mara aikin yi kuma wanda bai bincike kafin ya fara zargi

Lawal Muhammad Gusau, mai rajin kare hakkin dan Adam mazaunin garin Abuja, ya zargi jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayooyi da safarar yara.

A takardar korafin da Malam :Lawal Gusau ya fitar a ranar 25 ga watan Disamban 2020, ya ce jarumar ta kware a fataucin kwayoyi da fasa kwabrin yara.

A cewar Gusau, Nafisa ta mallaki kamfaninta mai suna Nafs Entertainment One Dream kuma yana da rijista ne a matsayin na nisahadantarwa, kamar yadda Kannywood Exclusive ta wallafa.

Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi
Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi. Hoto daga Kannywood Exclucive
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri

Tana kuma amfani da kamfanin wurin shigar da yara marasa gata a cikin fina-finai a bisa binciken da suka yi.

Miyagun kwayoyin da ake zargin jarumar da fataucinsu sun hada da: Benylin, Codeine, Pantazocine da Tramadol.

Har ila yau, Malam Gusau ya zargi jarumar da fakewa da tafiye-tafiye zuwa Turai inda take tunkaho da fim din da take yi.

Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi
Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi. Hoto daga Kannywood Exclusive
Asali: Facebook

KU KARANTA: Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

Amma hakikanin gaskiya shine ba bahaushiya bace, wata kabila ce mai suna Birom da ke Filato.

Ya nuna takaicinsa da yadda ta yi watsi da al'adun Malam bahaushe a kowanne ala'amari nata.

A yayin da Kannywood Exclusive ta tuntubi jarumar a kan abinda za ta iya cewa kan zargin nan, sai tace "Me kuwa zan ce? dama akwai mutane marasa aikin yi haka a duniya? Bani da kamfani mai wannan sunan."

Jarumar ta ce mahaifinta cikakken dan Kano ne kuma mahaifiyarta 'yar Jos ce ba Birom ba.

Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi
Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi. Hoto daga Kannywood Exclusive
Asali: Facebook

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda Janar Olu Bajowa mai ritaya ya ceci rayuwarsa inda ya tsallake mutuwa daga hannun Buka Suka Dimka a juyin mulkin 1976.

Obasanjo ya ce da Bajowa bai gayyacesa sunan dan sa ba, da tuni sojoji masu juyin mulki sun hallaka shi har lahira.

Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020 a jihar Ondo yayin bikin murnar cikar Bajowa shekaru 80 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel