Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri

Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri

- Majalisar wakilan Najeriya ta soke gayyatar da ta yi shugaba Buhari zuwa gaban majalisar

- Bayan soke gayyatar a kan rashin tsaro, majalisar ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri

- Majalisar ta yi hakan ne ganin cewa lamarin ya koma na kabilanci da kuma addini a cikinsu

A halin yanzu, majalisar wakilai bata da bukatar ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa a kan matsalar tsaro da ya addabi fadin kasar nan, jaridar The Nation ta tabbatar da hakan a ranar Asabar.

Shugaban majalisar kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, ya gano cewa gayyatar farko ta koma ta kabilanci da siyasa.

An gano cewa wasu 'yan majalisar da suka assasa gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bai wa fadar shugaban kasan hakuri.

KU KARANTA: Da duminsa: A lokaci daya 'yan Boko Haram suna kai hari a kauyuka 3 na Borno

Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri
Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Sun yi ikirarin cewa bukatar da suka mika ba su yi ta domin tozarta shugaban kasa ba, akasin yadda wasu suka kalla.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bukaci gaggawar daukar mataki daga fadar shugaban kasan bayan kisan manoma 48 na Zabarmari da ke jihar Borno.

Wadanda suka bukaci matakin gaggawar sun hada da: Hon. Ahmed Satomi, Hon. Mohammed Tahir Monguno, Hon. Zainab Gimba, Hon. Muktar Betara, Hon. Mallam Bukar Gana, Hon. Haruna Mshelia, Hon. Ahmadu Usman Jaha, Hon. Ibrahim Mohammed Bukar, Hon. Usman Zannah da Hon. Abdulkadir Rahis.

KU KARANTA: Hotunan gwamnan APC sanye da kayan soja a cikin daji yana cin abinci tare da dakaru

A wani labari na daban, A kalla mutum bakwai da suka hada da 'yan sa kai biyu suka mutu bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a kasuwar mako ta Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Samuel Aruwan, kwamishinan cikin gida ya sanar a ranar Alhamis, 'yan ta'addan sun shiga kasuwar wurin karfe 4 na yammacin ranar Laraba kuma suka bude wa jama'a wuta.

Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe kamar haka: Yusuf Magaji Iyatawa, Dabo Bafillace, Danjuma Haladu, Shuaibu Isyaku, Isyaku Adamu, Shehu Dalhatu da Musa Haruna Kerawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel