Hotunan ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a kan hanyar Kaduna
- Sojin Najeriya sun ragargaza wasu 'yan bindiga 9 a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna
- Hakan ta faru ne bayan bayanan sirrin da dakarun suka samu na wuucewar 'yan ta'addan
- Sojin sun yi kwanton bauna inda suka ragargaza 'yan ta'addan da suke wucewa da shanu
Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 9 a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin da suka yi musayar wuta da su a daren Litinin zuwa sa'o'in farkon ranar Talata, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar.
Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya sanar, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri ne da ke nuna cewa 'yan ta'addan suna kokarin matsawa daga yankin gabas na titin Abuja zuwa Kaduna zuwa yammaci tare da shanun da suka sata.
"Makiyayan wadanda aka sacewa shanun ne suka sanar da dakarun sojin inda suka dauka mataki," Aruwan yace a wata takarda da ya fitar ranar Talata.
KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila
Ya ce dakarun sun yi kwantan bauna har zuwa lokacin da barayin suka je wucewa sannan suka yi musu ruwan wuta, HumAngle ta wallafa.
Kwamishinan ya kara da cewa bayan ruwan wutar, sojin sun samu harsasai, kayan sojoji, takalman sojoji, barguna bakwai, wayoyi biyu, kaftani daya da igiyoyin daure shanu.
A safiyar Talata, an sake samun gawar daya daga cikin 'yan ta'addan, matattun shanu 16 da wasu uku da suka raunata.
Kamar yadda ya sanar, wasu 'yan ta'adda bakwai sun mutu sakamakon tsananin wutar harsasai da suka sha sannan wasu sassan jikinsu duk ya fita.
Aruwan ya ce har a yanzu dakarun sojin suna cigaba da sintiri a yankin.
KU KARANTA: Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar
A wani labari na daban, an kashe shugaban kungiyar mafarauta na jihar Adamawa, Young Mori, a wata musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda iyalansa da wasu majiyoyi suka tabbatar.
Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyata don kokarin yaki da 'yan ta'adda a jihohin arewa. Shugaban kungiyar, Salihu Wobkenso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, an kashe Mori ne a Kaduna. "Wannan mummunan labari ne ga mafarautanmu. Young Mori, daya daga cikin jaruman mafarautan jihar Adamawa daga karamar hukumar Guyuk ya riski ajalinsa a jihar Kaduna. Masu kiwon shanu sun kashe shi da safiyar yau."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng