Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)

Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)

- Lilian Mwangi na mamakin yadda jama'a suka dage suna yi wa mijinta ba'a

- A gareta, Mwangi Wawira shine namiji daya tilo da take so ta kare rayuwarta da shi

- Ma'auratan sun janyo cece-kuce bayan hotunan bikinsu ya karade kafafen sada zumunta

So gamon jini Hausawa ke cewa kuma baya duba asali, kyau, kudi ko wani banbanci na rayuwa. Abubuwan da so ya kan duba shine dabi'a, yanayin masoyin, kankan da kai, juriya, saukin hali da sauransu da idanuwa basu iya kallo.

A yayin da wasu ke gaggawar fadawa aure saboda sha'awa, wasu suna daukar dogon lokaci wurin samun cikakkiyar yarda da juna, hakuri da kuma soyayya mai wuyar tarwatsawa.

A lokacin da hotunan Lilian Mwangi da angonta suka fada kafafen sada zumuntar zamani, jama'a suna ta dariya tare da sharrance gajeren mijinta.

Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)
Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna). Hoto daga Lilian Mwangi
Source: Facebook

KU KARANTA: Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

Angon kusan tsawonsa rabin matar ne, lamarin da yasa maza suka sha alwashin ba za su taba yin irin wannan auren ba.

Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)
Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna). Hoto daga Lilian Mwangi
Source: Facebook

Amma kuma, waye ya kafa dokar nan ta cewa dole sai miji ya fi mata tsayi? Wadannan tambayoyin ne jama'a suka dinga yi.

Lilian ta ce tana kaunar angonta Mwangi Wawira a yadda yake. A takaice tana matukar farin cikin haduwarsu a shekaru hudu da suka gabata kuma yanzu suka angwance.

Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)
Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna). Hoto daga Lilian Mwangi
Source: Facebook

Masoyan sun yi aure a 2020 inda Lilian tace "Muna farin ciki kuma muna shan amarcinmu. Soyayya babu ruwanta."

KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila

A wani labari na daban, wata kotun kasar Saudi Arabia a ranar Litinin ta yanke wa wata Loujain al-Hathloul, daya daga cikin fitattun mata masu rajin kare hakkin mata shekaru biyar da wata takwas a gidan yari.

Kamar yadda rahotanni daga The Washington Post suka bayyana, 'yar gwagwarmayar an yanke mata hukunci ne a kan wasu laifuka da ke da alaka da ta'addanci, takarda daga 'yan uwanta ta tabbatar.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce zargin da ake yi mata duk a kan Hathloul na gwagwarmaya ne. Bukatar ta kawo karshen mulkin mallaka da maza ke yi a kan mata a kasar ne ya ja mata hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel