Kogi: Yahaya Bello ya yi ikirarin ‘bogi’ a kan gwajin da kamuwa da COVID-19

Kogi: Yahaya Bello ya yi ikirarin ‘bogi’ a kan gwajin da kamuwa da COVID-19

-Yahaya Bello ya yi ikirarin babu wanda ya kamu da Coronavirus a Kogi

-Gwamnan ya na da’awar cewa ana yi wa mutane gwajin cutar a jiharsa

-Alkaluman da su ka fito daga NCDC sun nuna mana haka abin yake

Duk da hujjoji baro-baro da ke nuna karancin gwajin COVID-19 tamkar rana a lokacin sallar azahar, gwamnan Kogi ya na ikirarin babu wanda ya kamu.

Bayan haka gwamna Yahaya Bello ya na da’awar cewa jami’ai sun dage da yi wa mutanen jihar Kogi gwaji domin gano masu dauke da kwayar Coronavirus.

Gwamnan ya hakikance a kan cewa cutar COVID-19 ba ta shiga Kogi ba. Premium Times ta ce da aka yi hira da shi a Channels TV, ya kara maimaita wannan.

“A jihar Kogi, mun ce ba mu da COVID-19, kuma hakikanin magana ita ce, ba mu da COVID-19.”

KU KARANTA: Buhari waliyyi ne inji Gwamna Bello

A cewar Bello, jami’an NCDC sun shiga ma’aikatu, kasuwanni, tasha, kan titi, kauyuka da birane su na gwaji, amma duk da haka babu wanda aka samu da cutar.

Bello ya kara da cewa: “Lokacin da aka koma makaranta, an yi wa ‘yan gari da wadanda ba ‘yan gari ba gwaji, kuma ba a samu wanda ya kamu da cutar ba.”

Bayan haka a cewarsa, NCDC ta yi wa duka masu bautar kasa na NYSC, (kusan mutum 700) da ke sansanin Kogi gwajin cutar, ya ce a nan babu wanda ya kamu.

Premium Times ta ce ba gaskiya gwamnan ya fada ba, zuwa ranar 11 ga watan Disamba, alkaluman COVID-19 ya nuna mutane 425 rak aka yi wa gwajin cutar.

KU KARANTA: Siyasa: A rika damawa da mata - Yahaya Bello

Kogi: Yahaya Bello ya yi ikirarin ‘bogi’ a kan gwajin da kamuwa da COVID-19
Gwamna Yahaya Bello Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Masana su na alakanta karancin masu cutar a Kogi da rashin yi wa mutane da-dama gwaji.

Alhaji Yahaya Bello ya saba sukar yadda ake kokarin yaki da Coronavirus a Najeriya, wanda hakan ya hada shi fada da hukumomi da jami’an lafiya na kasa.

Amma Bello ya ce bayan samun sabani da jami’an lafiya, daga baya ya kyale a rika yi wa mutane gwaji, inda aka yi wata daya ba a samu wani mai COVID-19 ba.

Idan za ku tuna, a lokacin da jami'an NCDC su ka isa Kogi, Yahaya Bello ya bukaci ma'aikatan lafiyan su killace kansu na kwanaki 14 ko su tattara su bar jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel