Gwamna Yahaya Bello ya bukaci a dinga saka mata a siyasa

Gwamna Yahaya Bello ya bukaci a dinga saka mata a siyasa

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yayi kira ga gwamnati da ta baiwa mata dama

- A cewar gwamnan, ya kamata a dinga bai wa mata manyan mukamai ana damawa dasu

- Ya ce jam'iyyar APC ta jihar Kogi za ta bai wa mata damar tsayawa takarar kansiloli

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bukaci gwamnati ta bai wa mata damar shiga harkar mulki, don a dama dasu.

A cewarsa, gwamnatinsa ta bai wa mata dama a matsayi daban-daban. Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, yayin tattaunawa da NGWA-GBV a Abuja.

A wata takarda wacce wakilin Legit.ng ya gani, inda kakakin gwamnan, Onogwu Mohammed, ya gabatar wa da manema labarai, wacce gwamnan yace ya aiwatar da duk abubuwan da yake shawartar sauran gwamnoni su yi.

Ya ce ya kafa tarihin zama gwamna na farko da ya zabi mace matsayin ADC ga gwamna, wanda hakan zai zama daya daga cikin hanyoyin daidaita jinsi a Najeriya.

KU KARANTA: Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki

Gwamna Yahaya Bello ya bukaci a dinga saka mata a siyasa
Gwamna Yahaya Bello ya bukaci a dinga saka mata a siyasa. Hoto daga @LuagrdHouse
Asali: Twitter

Ya kuma kara bayar da misalin yadda ya daura SSG da HOS dukansu mata, duk a karkashin mulkinsa.

Gwamna Bello ya kara da cewa ya daura mata da dama a mukamai manya-manya. Ya ce a zaben kananun hukumomi 12 da za a yi a jiharsa, an shirya da jam'iyyar APC a kan za ta bai wa mata dama 35% musamman wurin tsayawa takara.

Gwamnan ya ce a kowacce karamar hukuma akwai a kalla gundumomi 10 zuwa 15, za a baiwa a kalla mata 3 zuwa 4 a kowacce karamar hukuma damar tsayawa takarar kansila, don bai wa mata kwarin guiwa, don su san ana damawa dasu.

KU KARANTA: Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, inda ya shawarcesa da ya fatattaki kaf ministoci da hadimansa don sun gaza yin ayyukansu yadda ya kamata.

Ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Lafia, lokacin da ya kai gaisuwa ga Gwamna Abdullahi Sule a gidan gwamnati da iyalansa bisa rashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Mr. Philip Tatari Shekwo wanda 'yan bindiga suka kashe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng