PDP ta hadu da babban cikas yayinda jiga-jiganta suka koma APC a Nasarawa

PDP ta hadu da babban cikas yayinda jiga-jiganta suka koma APC a Nasarawa

- Jam’iyyar APC mai mulki ta tarbi wasu manyan jiga-jigan PDP a jihar Nasarawa

- Masu sauya shekar sun rataya hukuncinsu na sauya sheka a kan ci gaban da aka samu a jihar karkashin Gwamna Sule

- Usman Labaran, daya daga cikin masu sauya shekar zuwa APC, ya bukaci mazauna jihar da su ba gwamnatin goyon baya

Sansanin Peoples Democratic Party (PDP) na ci gaba da raguwa yayinda wasu jiga-jiganta suka sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Nasarawa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda suka sauya shekar sun hada da tsohon mamba mai wakiltan Toto/Gadabuke a majalisar jihar, Madaki Ada-Goje da kuma tsohon mai gudanarwar ci gaban yankin Gadabuke, Benjamin Musa Belodu da magoya bayansu.

KU KARANTA KUMA: Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah

PDP ta hadu da babban cikas yayinda jiga-jiganta suka koma APC a Nasarawa
PDP ta hadu da babban cikas yayinda jiga-jiganta suka koma APC a Nasarawa Hoto: @officialaasule
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, shine ya tarbi masu sauya shekar a yayin taron karshen shekara na masu ruwa da tsaki a APC wanda aka gudanar a karamar hukumar Toto.

Ya ce:

“Kokarin gwamnatin APC wajen inganta tsaro a yankin, samar da hannun jari a fannin noma, ba yan asalin jihar mukaman siyasa da sauransu ne suka sanya su sauya sheka daga PDP zuwa APC.

“Ina ba magoya bayanmu da wadanda ke adawa tabbacin cewa gwamnati ta dauki alkawarin wanzar da ci gaba domin jam’iyyar ta ci gaba har bayan zaben 2023.”

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo

A wani labarin, wata kungiya ta yi zargin cewa mambobin majalisar dokokin tarayya na shirin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da take magana ta wani jawabi a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, kungiyar, Core All Progressives Congress Supporters Network (Co-APC-SuN), ta bayyana kulla kullan a matsayin “ba abun yarda ba, abun bankyama, tozarci kuma abun Allah wadai.”

Ta kuma yi kira ga tsige Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya kuma kasance shugaban NASS na tara, jaridar The Sun ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel