‘Yan Majalisa sun mikawa Buhari kundin kasafin kudin 2021 domin ya sa hannu, shiru

‘Yan Majalisa sun mikawa Buhari kundin kasafin kudin 2021 domin ya sa hannu, shiru

- ‘Yan Majalisa sun gama aiki a kan kasafin kudin shekara mai zuwa

- An mikawa Shugaban kasa kudin kasafin tun kwanaki, ya sa hannu

- Har zuwa yanzu Muhammadu Buhari bai rattaba hannunsa a kai ba

Yayin da sa’o’i kusan 78 kacal su ka rage a shekarar nan ta 2020, har yanzu shugaban Najeriya bai rattaba hannunsa a sabon kasafin kudin kasar ba.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa kwanaki da mikawa shugaba Muhammadu Buhari kundin kasafin 2021, har yau bai sa hannunsa a kai ba.

Nawar da ake samu daga shugaban kasa zai jawo matsala wajen batar da kudin kasa, wanda aka yi nasarar dawo da shi tsarin Junairu-Disamba a 2020.

Rahotanni sun bayyana cewa an matsawa shugaba Buhari lamba, ya sa hannu a kasafin na badi.

KU KARANTA: Majalisa ta raina abin da aka warewa Arewa maso Gabas

A shekarar bara, Mai girma Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin 2020 ne tun a ranar 17 ga watan Disamban 2019, kafin shekara ta kare.

Wancan lokaci shugaban kasar ya sa hannu ne kwanaki 12 bayan majalisar tarayya ta dawo masa da kundin kasafin, bayan tsawon watanni ta na aiki.

Wannan karo kuwa, ‘yan majalisa sun karkare aiki a kan kasafin kasar ne a makon da ya gabata, inda su ka amince a kashe N13.58tr a shekarar da za a shiga.

Tun a wancan lokaci aka kai wa shugaban kasar kundin kasafin domin ya sa hannu, amma har yanzu bai yi ba, ya na mai cewa ya na lura ne da kundin.

KU KARANTA: Za ayi Kirismeti kamas-kamas, Gwamna ya ce babu albashi

‘Yan Majalisa sun mikawa Buhari kundin kasafin kudin 2021 domin ya sa hannu
Buhari a Majalisa Hoto: Twitter/ @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Idan ana so a cigaba da tafiya a wannan tsari na Junairu zuwa Disamba, dole shugaban kasa ya sa hannu a kan kasafin kudin tsakanin Talata zuwa Alhamis.

Kwanakin baya kun ji cewa sabon kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na 2021 ya tabbatar da tafiyar kudin tallafin man fetur a Najeriya.

A cikin kasafin kudin na shekara mai zuwa, babu inda gwamnatin tarayya ta nuna cewa za ta janye karin kudin fetur da na shan wutar lantarki da ta yi.

Sannan gwamnati ba ta yi bayanin yadda za a kara albashin Malamai da aka yi alkawari ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng