Adingi: Abin da ya sa Jihar Benuwai ba za ta iya biyan albashin Disamba ba
- Ma’aikatan gwamnatin Benuwai ba za su samu albashi a Disamban nan ba
- Ngunan Adingi ta ce dalilin haka shi ne wasu kotu sun ce a rufe asusun jihar
- Gwamnatin Benuwai ta na ta faman shari’a da wasu ma’aikatanta tun 2007
Ma’aikatan gwamnati a jihar Benuwai za su yi bikin kirismeti ba tare da sun samu albashi ba.
Da ta ke bayanin dalilin da ya sa ba a biya ma’aikatan gwamnati albashin watan Disamban nan ba, Ngunan Adingi ta ce an rufe asusun gwamnatin jihar.
Kwamishinar harkokin yada labarai, al’adu da shakatawa ta Benuwai, Misis Ngunan Adingi ce ta yi wa ‘yan jarida wannan karin-haske a ranar Alhamis.
Jaridar Punch ta rahoto Adingi tana kokawa a kan yadda Alkalin kotu ya jawo abubuwa su ka tsaya cak a gwamnatin bayan bada umarnin rufe asusunta.
KU KARANTA: ‘Dan shekara 44 da aka kama da laifin satar yarinya zai tafi kurkuku
Kwamishinar ta ce wasu mabanbantan kotu a Nasarawa da garin Abuja ne su ka bada hukunci a kan gwamnati, bayan wasu ma’aikata sun kai jihar kara.
“Wasu wadanda ba ‘yan jiha ba da su ka yi aiki a nan da aka maida zuwa wuraren aikinsu a 2007, a tsarin SUBEB, sun kai gwamnati kara.” inji Misis Adingi.
“A dalilin haka a 2008, a shari’ar Juliana Igweka da wasu mutane da kuma bangaren SUBEB da gwamnatin Benuwai, kotu ta ce a maida su wurin aikinsu.”
A cewar kwamishinar, bayan wadannan ma’aikata sun yi nasara a kotu, sai su ka koma su na neman a biya su kudi, abin da ba shi Alkali ya zartar ba.
KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Tarayya za ta haramta wasu mutane barin Najeriya
"Bayan sun gagara sa kotu ta yi abin da su ke so, sai su ka tafi kotu a Nasarawa da FCT, su ka sa a toshe asusun gwamnati, wanda aka bada umarni ayi jiya.”
“Wannan ya jawo aka tsaida duk aikace-aikace gwamnati, har da biyan albashi.” Inji Kwamishinar.
Dazu kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin cewa babu wani wanda zai taka kafa ya zo Aso Villa yawon Kirismeti a shekarar bana.
Yayin da ake gobe Kirismeti, shugaban Najeriyar, Buhari ya fitar da jawabi ya ce babu maganar ziyarar da aka saba a shekarar nan saboda annobar COVID-19.
Buhari ya ba mutane shawarar su bi sharuda da dokoki, sannan su hakura da yawan tafiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng