Kasar Saudiyya ta haramta aure da aurar da kananan yara

Kasar Saudiyya ta haramta aure da aurar da kananan yara

- Mahukunta a kasar Saudiyya sun tsayar da shekaru goma sha takwas a matsayin mafi karacin shekarun aure

- A wata takardar mai dauke da sa hannun ministan shari'a kuma shugaban kotunan Saudi, an umarci kotunan kasar su fara aiki da dokar

- An dade ana muhawara a kan mafi karancin shekarun aure ko aurar da 'yammata kafin kasar Saudiyya ta dauki wannan mataki

Ma'aikatar Shari'a ta ƙasar Saudiyya ta haramta aure ko aurar da ƴammata 'yan ƙasa da shekara goma sha takwas da haihuwa.

Kazalika, gwamnatin kasar ta kuma saka dokar shekara 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da za'a yi aure.

Ministan Shari'a kuma Shugaban kotunan ƙasar, Sheik Walid Al-Samaani, shine ya bada sanarwar dokar ga duk kotunan da ke faɗin ƙasar Saudiyya.

Acewar Jaridar Premium Times, auren ƙananan yara mata a saudiyya abune da aka saba.

KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri

A cikin yara mata bakwai, ɗaya daga cikinsu ta na aure kafin cika shekaru 18.

Kasar Saudiyya ta haramta aure da aurar da kananan yara
Kasar Saudiyya ta haramta aure da aurar da kananan yara @Vanguard
Source: Twitter

Amma ministan Shari'a na ƙasar Saudiyya na shirin sauya lamarin.

A makon da ya gabata ne Injiniya Muneer Al-Jundi, mutumin da ya kera tare da jagorantar gina kofar dakin Ka'aba ya rasu, yadda Legit.ng ta wallafa.

Daily Trust ta rawaito cewa hukumar kula da Masallatan Haramain da ke kasar Saudia ne ta sanar da mutuwar Injiniya Muneer.

Sanarwar ta bayyana cewa Injiniya Muneer ya rasu ne ranar Laraba a birnin Stuttgart na kasar Jamus.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Hukumar Masallatan Haramain ta yi addu'ar Allah ya yi masa gafara da rahama.

Injiniya Muneer ne ya zana fasalin sabuwar kofar dakin Ka'aba da aka kera da ruwan zinare shekara 44 da suka wuce.

Khalidi bin Abdul Aziz, sarkin Saudi a wancan lokacin, shine ya zabi Injiniya Muneer daga kamfanin Sheik Mahmud bin Badr domin ya jagoranci kera kofar.

Kamfanin Injiniyarin na Sheikh Mahmud bin Badr ya yi suna wajen fitar da taswira da kere-kere da ruwan zinare.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel