Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri

Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri

- Kingsley Chinda, mamba a majalisar wakilai, ya tofa albarkacin bakinsa a kan matsalar rashin tsaro da batun neman a tsige Buhari

- A kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana cewa za'a hukunta dan majalisar saboda kiran a tsige Buhari

- Bayan ya bayyana dalilin fushinsa da shugaba Buhari, Chinda ya bukaci mambobin majalisa su saka jama'a a zuciyarsu

Mamba a majalisar wakilai, Kingsley Chinda, ya ce akwai maganar shirye-shiryen fara tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a zauren majalisa.

Dan majalisar ya bayyana cewa shi da wasu mambobin majalisa sun fara wayar da kan abokansu domin su amince a tsige Buhari, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Chinda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shi a wani gidan Radion FM da ke kan mita 92.3 a Fatakwal, jihar Ribas.

KARANTA: Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya

Kazalika, ya mayar da martani a kan kiran da ginshikin majalisa, Alhassan Ado Doguwa, ya yi na neman a hukunta shi saboda kiran a tsige Buhari.

Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri
Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

"Muna tattauna wa da abokanmu kuma muna tuntubar 'yan Nigeria kuma muna karfafawa 'yan kasa gwuiwar su yi magana da mambobin da ke wakiltarsu. Idan jama'ar mazabar Doguwa suka ce masa muna son ka saka hannu a kan takardar tsige shugaban kasa, bashi da wani iko na kin goya musu baya," a cewarsa.

Honarabul Chinda ya zargi shugaba Buhari da gaza sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya rataya masa na tabbatar da tsaro a Nigeria.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, ya ce sai mutanen yankin kudu maso gabashin kasar nan, na 'yan kabilar Igbo, sun sauya halayyarsu kafin su samu takarar kujerar shugaban kasa.

Sanata Anyim, ya yi wannan iƙirari ne a wani biki mai taken World Igbo Summit, wanda jami'ar Gregory dake Uturu a jihar Abia ta shirya a karo na shida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Cikin bayaninsa mai taken, "Duban tsanaki kan buƙatar ƙabilar Igbo ga mulkin ƙasar nan tare da tsarin cimma hakan," Anyim ya nuna giɓin dake akwai na ɓallewa ko sauya tsarin fasalin ƙasar nan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel