Injiniya Muneer: Mutumin da ya kera kuma ya jagoranci gina kofar Ka'aba ta gwal ya rasu

Injiniya Muneer: Mutumin da ya kera kuma ya jagoranci gina kofar Ka'aba ta gwal ya rasu

- Shekaru arba'in da uku kenan tun bayan da tsohon sarkin Saudia, Khalidi bin Andul Aziz, ya sauya kofar dakin Ka'aba

- Ya bayar da aikin kera sabuwar kofar ne ga kamfanin Injiniyarin na Sheikh Muhammad bin Badr

- Injiniya Muneer Al-Jundi ne ya kera kofar tare da jagorantar gina ta a wancan lokacin

Injiniya Muneer Al-Jundi, mutumin da ya kera tare da jagorantar gina kofar dakin Ka'aba ya rasu, yadda Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta rawaito cewa hukumar kula da Masallatan Haramain da ke kasar Saudia ne ta sanar da mutuwar Injiniya Muneer.

Sanarwar ta bayyana cewa Injiniya Muneer ya rasu ne ranar Laraba a birnin Stuttgart na kasar Jamus.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Hukumar Masallatan Haramain ta yi addu'ar Allah ya yi masa gafara da rahama.

Injiniya Muneer ne ya zana fasalin sabuwar kofar dakin Ka'aba da aka kera da ruwan zinare shekara 44 da suka wuce.

Injiniya Muneer: Mutumin da ya kera kuma ya jagoranci gina kofar Ka'aba ta gwal ya rasu
Injiniya Muneer: Mutumin da ya kera kuma ya jagoranci gina kofar Ka'aba ta gwal ya rasu @Daily_trust
Asali: Twitter

Khalidi bin Abdul Aziz, sarkin Saudi a wancan lokacin, shine ya zabi Injiniya Muneer daga kamfanin Sheik Mahmud bin Badr domin ya jagoranci kera kofar.

Kamfanin Injiniyarin na Sheikh Mahmud bin Badr ya yi suna wajen fitar da taswira da kere-kere da ruwan zinare.

KARANTA: Covid-19: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai da Coci

Kofar dakin Ka'aba da Injiniya Muneer ya kera tana da nauyin kilogram 280 Kuma an shafe shekara guda ana aikinta.

A shekarar 1970 Sarki Khalidi ya bawa Injiniya Muneer aikin kera sabuwar kofar bayan wacce aka saka zamanin sarki Abdul Aziz ta tsufa.

Tun a wancan lokacin, shekaru 43 baya, aka karrama Injiniya Muneer ta hanyar rubuta sunansa a jikin kofar.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa cewa Allah ya yiwa Farfesa Habu Shuaibu Galadima, shugaban cibiyar NIPSS, rasuwa.

Darekta a NIPSS, C. F. J Udaya, ne ya sanar da mutuwar Farfesa Galadima a cikin wani sako da ya wallafa da yammacin ranar Lahadi

Ya ce marigayi Farfesa Galadima ya yi mutuwar fuj'an da safiyar ranar Lahadi bayan takaitacciyar rashin lafiya

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng