'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP, Adamu Mohammed, sun yi awon gaba da 'ya'ayansa 'yammata uku

'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP, Adamu Mohammed, sun yi awon gaba da 'ya'ayansa 'yammata uku

- Ahmodu Mohammed, shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Kampala a Bosson, jihar Neja, ya rasa ransa sakamakon harin 'yan bindiga

- Wasu 'yan bindiga, kimanin su goma sha biyar, sun kai hari gidan Mohammed da tsakar daren ranar Juma'a

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'yammata uku, 'ya'yan Mohammed, bayan sun kashe shi

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kashe wani mutum da aka bayyana sunansa da Ahmodu Mohammed, shugaban jam'iyyar PDP mazaɓar Kampala dake karamar hukumar Bosson jihar Niger.

Bugu da ƙari, bayan maharan sun kashe marigayin, ana kuma zargin sun sace yayan sa mata uku sun tafi da su kamar yadda rahoton jaridar TheCable ya bayyana.

A ranar Alhamis da ta gabata ne maharan, wadanda aka ce adadinsu ya haura mutum 15, suka kashe Mohammed bayan da suka kutsa kai cikin gidansa da misalin ƙarfe 2 na dare.

KARANTA: Majalisa na gab da zartar da doka mai tsauri a kan masu noma, sayarwa da shan tabar wiwi

Wannan na faruwa ne bayan hari biyu da mazauna yankin suka ce maharan sun kawo yankin nasu inda suka bayyana takaicinsu kan rashin tsaron da ke neman addabar yankinsu.

'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP, Adamu Mohammed, sun yi awon gaba da 'ya'ayansa 'yammata uku
'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP, Adamu Mohammed, sun yi awon gaba da 'ya'ayansa 'yammata uku @Thecable
Asali: Twitter

TheCable ta rawaito ce tuni majiyarta ta tabbatar mata da cewa tuni aka binne marigayi Mohamed bisa tsarin addinin Musulunci.

Duk ƙoƙarin da gidan jaridar TheCable ta don jin ta bakin Wasiu Abiodun, kakakin rundunar yan sandan jihar Niger, ya ci tura, haka ma bai bada amsar sakon kar-ta-kwana da ta aike masa ba.

KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri

Ana cigaba da samun ƙaruwar kai hare-hare a jihar Niger cikin yan kwanakin nan.

Rahoton kisan Mohammed na zuwa ne kwanaki kaɗan da kaiwa ƙauyen Madaki dake ƙaramar hukumar Rafi hari, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku a ranar 20 ga watan Disamban da muke ciki.

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta rawaito cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.

Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng