Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari

Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da bakin ciki da yake shiga idan aka samu rashin tsaro

- Ya ce kamar yadda iyaye da marikan yara ke jin takaici, haka yake shiga tashin hankali idan aka samu karantsayen tsaro

- Ya yi kira ga masu kishin kasa da taimaka wa sojoji wurin samar musu da bayanan sirri don kawo karshen rashin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan.

KU KARANTA: Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa

Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari
Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Na kan shiga halin damuwa fiye da matasa. A yanzu an fi saka wa 'yan makaranta ido kuma 'yan ta'addan nan suna mayar da su hanyar tada hankulan al'umma.

"A matsayina na uba, ina samun tashin hankali tare da alhinin da iyaye tare da marika ke shiga idan yaransu suka fada hannun makiyan al'umma.

"Ina rokon sauran masu kishin kasa da su bai wa dakarun soji da sauran hukumomin tsaro goyon baya da hadin kai ta hanyar samar da bayanan sirri domin kakkabe dukkan 'yan ta'adda da ke damunmu," wani sashi na takardar ya sanar.

Ya dauka alwashin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bai wa dakarun soji dukkan goyon baya da suke bukata, Daily Trust ta wallafa.

Ya horesu da su mayar da hankali wurin kawo karshen rashin tsaron da ya addabi jama'a.

KU KARANTA: Duba cikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan mai AC, wurin caji da bandaki kayatacce

A wani labari na daban, daga bakin wasu daga cikin yaran makarantar Kankara da aka sace, sun tabbatar da cewa an biya kudin fansa kafin a sakesu, mujallar The Wall Stree ta tabbatar.

Akasin ikirarin gwamnatin tarayya da cewa babu sisin kwabo da aka biya domin kubutar da dalibai 334 daga hannun 'yan bindiga.

A wani rahoton ranar Laraba, WSJ ta ce uku daga cikin daliban da aka sace sun tabbatar da cewa an biya kudi kafin a sakesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng