Abubuwa 10 da baka sani ba game da marigayi Sheikh Ahmad Lemu

Abubuwa 10 da baka sani ba game da marigayi Sheikh Ahmad Lemu

Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger. Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Daya daga cikin yayan marigayin, Maryam Lemu, ta tabbatar da mutuwar mahaifinsu a wata sanarwa a Facebook, ta ce idan anjima kadan za a soma shirye-shiryen binne shi.

Abubuwa 10 da baka sani ba game da marigayi Sheikh Ahmad Lemu
Abubuwa 10 da baka sani ba game da marigayi Sheikh Ahmad Lemu Hoto: Kingfaisalprize.org
Asali: UGC

KU KARANTA: An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

Ga jerin abubuwa da ya kamata ka sani game da shahararren malamin addinin:

1. An haifi Dr. Shaikh Ahmad Lemu a garin Lemu, jihar Neja ranar 21/12/1929.

2. Ya yi karatunsa na Qur'ani a 1932, firamare 1 1939, sakandare a 1948, kwalejin ilmin shair'a dake Lemu a 1950, sannan NCE Arabic a 1952.

3. A 1954, ya tafi jami'ar Landan a kasar Birtaniya inda yayi karatun tarihi, Hausa, da yaren Farisa a 1961, sannan ya samu digiri kan karatun nahiyar Afrika a 1964.

4. Ya karantar da dalibai na sama da shekaru 50 a rayuwarsa

KU KARANTA: FEC: Gwamnatin Tarayya za ta kashe N8bn a gyaran titunan da su ka lalacE

5. Duk da karantarwan da yake yi, ya kasance Alkali inda ya zama Alkalin kotun shari'a na farko a kotun daukaka karan Sokoto da Neja (1976 - 1977) sannan ya zama babban Alkalin jihar Neja (1976 - 1991)

6. Dr. Shaikh Ahmed Lemu ya auri baturiya, Aisha Lemu, kuma suna da yara da suka shahara wajen da'awar addinin Musulunci. Daga cikinsu akwai Sheikh Nurudeen Lemu da Malama Maryam Lemu.

7. Marigayin ya kasance mai da'awar addinin Musulunci inda ya kafa cibiyar 'Islamic Education Trust' (IET) mai hedkwata a Minna, jihar Neja.

8. Lemu ya samu kyaututtuka da lambar yabo da dama a rayuwarsa. Daga ciki ya samu lambar yabon jarumin kasa daga wajen shugaban kasan mulkin Soja, Abdus Salam Abubakar a 1999 da kuma lokacin shugaba Olusegun Obasanjo a 2001.

Hakazalika ya samu doktora na karamci daga jami'ar Danfodiyo a 1996, jami'ar Osun a 2011, da jami'ar Al-Hilal dake Masar a 2013.

(An samu bayanai a shafin lambar yabon King Faisal)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng