Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar

Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar

Shahrarren attajirin jihar Katsina, Dahiru Mangal, ya bada gudumuwar sama da motoci 100 ga yakin neman zaben tsohon minista, Mohamed Bazou, a jamhurriyar Nijar.

A wani bidiyon da PRNIgeria ta samu, attajirin ya bayar da motocin ne a garin Maradi, wacce ke da iyaka da Najeriya.

An yi rubutu “Mohammed Bazoum, 2021” a jikin motocin hade da hotunan dan takaran.

Dahiru Mangal wanda shine mammalakin kamfanin jiragen saman Max Air, na da arzikin da akayi kiyasi ya kai $765 million.

Ya kasance babban dan kasuwa, kuma masanin ayyukan masana'antu.

Wannan gudunmuwa da ya bayar zai karfafa yakin neman zaben Mohamed Bazoum, wanda shine dan takaran jam'iyyar Party for Democracy and Socialism (PNDS) kuma na hannun daman shugaban Nijar, Mohammed Issoufou.

Za'a gudanar da zaben ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba.

PRNigeria ta tattaro cewa idan wani dan takara bai samu kuri'u sama da rabin wadanda suka kada kuri'a ba, za'a yi sabon lale ranar 21 ga Febrairu, 2021.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona

Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar
Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar Hotuna: PRNigeria.com
Asali: UGC

Bazoum zai kara da yan takara 29, wanda ya hada da Mahamane Ousmane, wanda yayi shugabancin kasar daga 1993-1996; da eini Ooumarou, tsohon firam ministan kasar, dss.

Shugaba Mahamadou Issoufou zai sauka daga mulki shekaru 10 kan mulki.

KU KARANTA: Buhari ya aikewa Kwankwaso ta'ziyyar rasuwan mahaifinsa, Makaman Karaye

A wani labarin daban, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gurfanar da wasu ‘yanuwan juna da laifin yi wa Prince Arthur Eze.

Ana zargin Eze Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka da kamfanoninsu da laifin satar N1.5b daga uban gidansu, Prince Arthur Eze.

A jawabin da hukumar EFCC ta fitar, ta nuna cewa an gurfanar da Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka a kotun tarayya da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel