Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba

Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba

-Jama'a suna tamabayar ina babban Alkalin kotun koli ta Najeriya, Tanko Muhammad

- Tun bayan taron rantsar da alkalan kotun koli da yayi da kansa, ba a sake ganinsa ba a wani taro

- Rashin ganinsa ya janyo cece-kuce, inda ake ta rade-radin ba shi da lafiya an fitar dashi kasar waje

Mutane suna ta yada labaran cewa ba shi da lafiya, kansancewar bai bayyana a kotu ba ranar bikin rantsar da manyan lauyoyi 72 na Najeriya.

An dade ba a ganin babban alkalin, mai shekaru 66 a bainar jama'a. Taron da aka yi na rantsar da manyan lauyoyi, wanda aka yi shi a kotun koli ya dauki hankali kwarai.

Rashin ganin CJN a kotun ba abu bane wanda aka saba da shi, saboda shine yake gudanar da abubuwa da dama a ranar.

CJN ya rantsar da alkalan kotun koli guda 8 a ranar 6 ga watan Nuwamba, amma tun daga nan ba a ganin shi a cikin mutane.

Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba
Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta

Duk da dai bai bayar da wani dalili na rashin bayyanarsa ba, TheCable ta gano cewa ba shi da lafiya, kuma an fitar dashi kasar waje don nema masa lafiya.

Kafin a fitar da shi kasar waje, an samu rade-radin cewa ya kamu da wata cuta mai saurin yaduwa.

TheCable bata gano inda yake ba, kuma har ranar Litinin, babu wanda yake son bayar da labari a kansa.

KU KARANTA: Yadda ma'aikaci a ma'aikatar man fetur ya bai wa kansa kwangilar N145m

A ranar rantsarwar, ya samu wakilcin Bode Rhodes-Vivour, alkalin kotun koli, inda yace: "Fannin Shari'a, kamar sauran bangarori na gwamnati, ta fuskanci kalubale iri-iri na tsawon shekaru.

"A wasu shekaru, mun rasa abokan karatunmu, wadanda suka fi kusanci da mu. Alkali Karibi Whyte, JSC, CFR da Sylvester Umaru Onu, JSC, CON, sun mutu a ranar Juma'a, 23 ga watan Mayun 2020 da kuma Litinin 30 ga watan Nuwamban 2020.

"Sannan mun rasa manyan alkalan jihar Yobe da na Kogi, Alkali Garba Musa Nabaruma da Nasir Ajana.

"Cikin wannan kankanin lokacin, mun rasa shugaban kotun daukaka kara ta jihar Kogi, Alkali Jude Okeke na babbar kotun Abuja, tsohon babban alkalin jihar Neja, Jibrin Ndatsu Ndajiwo; alkalin jihar Legas mai murabus, Alkali Isiaka Isola Oluwa; Alkali Maikata Bako na babbar kotun jihar Katsina da kuma Alkali Fidelis Ngwu na jihar Enugu, da sauransu."

Ya shawarci rantsattsun lauyoyin a kan rikon gaskiya da amana, kuma ya horesu da kada su yi amfani da damarsu wurin saba wa dokokin kotu.

A wani labari na daban, kungiyar musulunci ta Najeriya, wacce Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, Sarkin Sokoto yake jagoranta ta ce ta samu mummunan labari wanda ya dimauta ta na satar daliban GSSS, Kankara, jihar Katsina, bayan harbin jami'an tsaron a bakin makarantar da misalin karfe 10:45pm a ranar Juma'a.

Dr. Khalid Abubakar Aliyu, babban sakataren JNI, a wata takarda, ya ce wannan daya ne daga cikin miyagun hare-haren da 'yan ta'adda suka kai, bayan kisan Zabarmari da ya auku babu dadewa, Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng