Omokri: Idan da sunan Sharibu ka samu $20, 000, ka je ban bukata inji Garba Shehu

Omokri: Idan da sunan Sharibu ka samu $20, 000, ka je ban bukata inji Garba Shehu

-An ce za a ba Hadimin Buhari $20, 000 idan ya kwana a kauye babu jami’ai

-Reno Omokri ya yi wa Garba Shehu wannan tayi, Hadimin bai iya dauka ba

-Garba Shehu ya zargi Remo Omokri da karbar kudi da sunan Leah Sharibu

A yanzu babu labarin da ‘Yan Najeriya su ke yi a dandalin sada zumunta da kafofin zamani irin martanin da Garba Shehu ya maidawa Reno Omokri.

Jiya Laraba da rana, Reno Omokri ya yi raddi a kan maganar da Garba Shehu ya yi na cewa an samu tsaro a karkashin shugaba Muhammadu Buhari.

Reno Omokri, fitaccen ‘dan adawa kuma tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jefawa Malam Garba Shehu wani kalubale.

Omokri ya kalubalanci Shehu ya kwana a kauyen Koshobe ko Kware, ya ce idan ya yi hakan, fam Dala $20000 su na jiransa ta hannun Cif Dele Momodu.

KU KARANTA: An kashe Matashin da ke NYSC a hanyar Abuja-Jere

Fasto Omokri ya yi kokarin ganin sai da mai magana da yawun bakin shugaban kasar Najeriyar ya ga wannan sako da ya aika masa a shafinsa na Twitter.

Malam Garba Shehu ya yi fatali da tayin da aka yi masa, ya ce sam ba zai karbi kudin ba, kuma ya zargi Omokri da cin kasuwa da ta’adin ‘Yan Boko Haram.

Shehu ya nuna cewa Fasto Omokri ya karbi makudan kudi da sunan Leah Sharibu, karamar yarinyar da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace a Dapci.

“Idan har kudin da ka tattaro ne daga gudumuwar da aka kawo da sunan Leah Sharibu, kiristar yarinyar da ta yi rashin dace Boko Haram su ka sace ta…”

KU KARANTA: Abin da Garba Shehu zai yi, in ba shi $20, 000 - Reno

Omokri: Idan da sunan Sharibu ka samu $20, 000, ka je ban bukata inji Garba Shehu
Garba Shehu Hoto: facebook/GarShehu
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasar ya ce: “To ko daga nesa ne, ba zan taba ba. Don Allah ka rike Dalarka $20,000”

Zuwa yanzu babu hujjar da Shehu ya bada da za ta nuna Omokri ya karbo kudi da sunan wannan Baiwar Allah, zargin da Omokri bai iya karyatawa ba.

‘Dan Majalisar Ribas, Kingsley Chinda ya ce ba zai nemi afuwa don ya fito ya na kiran a sauke Muhammadu Buhari daga kan kujerar shugaban kasa ba.

Jagoran ‘Yan jam'iyyar PDP maras rinjaye, ya hakikance a kan tsige shugaban kasa a Majalisar Wakilai, ya ce wannan shi ne matsayar PDP da 'ya 'yanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel